Toh fa: Mijina na kwanciya da mata masu tabin hankali - Matar aure ta fada wa kotu

Toh fa: Mijina na kwanciya da mata masu tabin hankali - Matar aure ta fada wa kotu

Wata kotun gargajiya da ke zamanta a Ado Ekiti, babban birnin jihar Ekiti, ta raba auren dake tsakanin wata mata mai suna Amaka da mijinta Friday Nwafor.

Kotun ta raba auren ne bayan Amaka, mai shekaru 37, ta shaida mata cewa mijinta, Nwafor, mai shekaru 47 na yin lalata da mata masu larurar tabin hankali.

Amaka, mazauniyar unguwar Oke-Bola, ta fada wa kotun cewa mijinta na yawan kyarar ta a bainar jama'a tare da zarginsa da rashin kula wa da ita.

Matar, mai 'ya'ya hudu, ta ce Nwafor na fake wa da yi wa mata masu tabin hankali addu'a domin ya yi lalata da su.

Ta kara da cewa daya daga cikin irin matan da yake lalata da su ta amsa da bakinta cewa ya kwanta da ita duk da ya san tana da miji. Amaka ta sanar da kotun cewa matar ta fadi hakan ne bayan ta samu lafiya.

Kazalika, Amaka ta sanar da kotun cewa tana cin amanar mijinta, saboda ba ya kula wa da ita baya ga yawan dukanta da ya ke yi koda kuwa tana dauke da juna biyu ne.

DUBA WANNAN: Kacibus: An kama gawurtaccen dan fashi da ake nema 'ruwa a jallo' a wani asibitin Katsina

A cewar ta, Nwafor ba ya bari ta amsa kiran kowa a waya, koda kuwa na mahaifiyarta ne, a saboda haka ta nemi kotun ta araba aurensu sannan ta tilasta Nwafor ya ziyarci iyayenta domin tattauna yadda za dauki dawainiyar yaran da suka haifa.

A nasa bangaren, Nwafor ya musanta dukkan zargin da Amaka ke yi masa tare da bayyana cewa matar tasa mazinaciya ce da ke barin gidansu na aure ta tafi gidan saurayinta ta shafe kwanaki a can.

Alkaliyar kotun, Uwargida Olayinka Akomolede, ta raba auren saboda yawan rikicin da ma'auratan ke yi da kuma gazawarsu wajen sulhunta banbancin da ke tsakaninsu.

Akimolede ta ce auren ya mutu har abada tare da bayyana cewa Amaka ta cigaba da rikon yaran da suka haifa, yayin da Nwafor zai ke biyanta kudin reno da abincin yara kowanne wata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel