Wani Bafaranshe ya kera injin tashi sama mai tsananin gudu

Wani Bafaranshe ya kera injin tashi sama mai tsananin gudu

- Wani Bafaranshen mutum ya kera wani inji mai tashi sama da mutum mai dan karen gudu

- Mutumin mai suna Franky Zapata ya shafe shekaru masu yawa yana bincike akan yadda zai kera wannan inji

- A ranar Lahadin nan da ta gabata ne Zapata ya samu nasarar tashi da injin nasa inda yayi tafiya mai nisan gaske dashi

Wani mutumi dan kasar Faransa ya shafe shekaru masu dumbin yawa yana bincike akan yadda zai kera wani inji da zai dinga tashi da mutum sama yayi tafiya mai nisa dashi, a karshe dai mutumin mai suna Franky Zapata ya kera injin wanda ya sanyawa suna Flyboard a turance.

Bafaranshen yayi nasarar tashi da injin a ranar Lahadin nan da ta gabata inda ya samu nasarar yin tafiya mill 22 a cikin sararin samaniy, yayin da wasu jirage masu saukar ungulu guda uku suka raka shi.

KU KARANTA: Kasar Amurka ta karrama jarumi Ali Nuhu

Ranar Lahadin da misalin karfe 8:17 Bafaranshen ya samu damar tashi da injin nasa, inda kuma yayi tafiyar kimanin mintuna 22 a sararin Subhana, daga baya kuma ya kara lulukawa tun daga kasarsa ta Faransa ya nufi kasar Birtaniya.

Rahotanni sun nuna cewa injin da Zapata ya kera yanayin gudun kilomita 160 zuwa 170 a cikin sa'a daya.

Shekaru goma dai da suka shude Zapata yayi nasarar tashi da injin nasa amma kuma cikin rashin sa'a sai ya fada cikin teku.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel