Ikon Allah: Kofura Bashir Umar wanda ya mayar da kudi N15m ya samu zuwa Hajji

Ikon Allah: Kofura Bashir Umar wanda ya mayar da kudi N15m ya samu zuwa Hajji

Jim kadan bayan karrama da karin girma da ya samu wajen babban hafsn sojin kasa, Jami'in hukumar sojin saman Najeriya, Kofura Bashir Umar, yana daga cikin mahajjatan Najeriya da ke gabatar da Ibada a hajjin Bana.

Legit.ng ta samu hoton Bashir Umar a cikin masallaci.

Kofura Bashir Umar, ya kasance dan agajin kungiyar Izalah kafin ya zama jami'in soja ya dawo da kudi Yuro 37,000, kimanin milyan 15 ga wani Alhaji Ahmed, wanda ya yarda kudin a ranar Talata, 16 ga watan Yuli, 2019 a kasuwan sansanin maniyyata aikin Hajji dake jihar Kano.

Ikon Allah: Kofura Bashir Umar wanda ya mayar da kudi N15m ya samu zuwa Hajji
Ikon Allah: Kofura Bashir Umar wanda ya mayar da kudi N15m ya samu zuwa Hajji
Asali: Facebook

KU KARANTA: Tafiya Indiya jinya: Ana shiryawa Zakzaky da matarsa sabon fasfot

Babban hafsan sojin saman Najeriya a ranar Alhamis a birnin tarayya Abuja ya karawa Bashir Umar, girma daga matsayin ACM zuwa Kofura. Ya bayyana cewa wannan zai zama darasi ga sauran jami'an hukumar da kuma nuna cewa hukumar sojin sama na masu gaskiya, aminci da mutunci ne.

Hakazalika shugaba Muhammadu Buhari ya yabawa Bashir Umar inda ya ce har yanzu akwai na'allah cikin al'ummar Najeriya duk da halin yunwa da kunci da ake ciki.

Kafura Bashir Umar ya bayyana cewa ko kodan bai yi nadamar mayar da kudin ga mai shi ba saboda mahaifinsa yayi masa tarbiyyar kada ya dauki abinda ba nasa ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel