Da na zauna da kishiya gara na kashe kaina – Inji wata Mata da mijinta zai kara aure

Da na zauna da kishiya gara na kashe kaina – Inji wata Mata da mijinta zai kara aure

Wata mata mai suna Sumayya Jafar ta yi kokarin kashe kanta da kanta ta hanyar rataya ba don komai ba sai domin kawai mijinta ya bayyana mata shirinsa na kara aure, kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.

Wannan lamari dai ya faru ne a gidan da ma’auratan suke zama dake unguwar Kuka mai Bulo cikin garin Kano, inda Sumayya ta yanke shawarar kashe kanta sa’annan ta daure wuyanta a jikin igiya da nufin aiwatar da abin da ta kudurta a ranta.

KU KARANTA: Duk da matsalar Boko Haram, NNPC za ta koma tafkin Chadi don hakar man fetir

A cewar Sumayya, ba za ta taba yarda ta zauna da kishiya ba, don kuwa da ta zauna da kishiya gara ma ta halaka kanta da kanta. Sai dai cikin ikon Allah bata kai ga mutuwa jami’an Yansanda suka ceceta.

A yanzu haka an garzaya da Sumayya zuwa wani asibiti dake garin Kano domin samun kulawar daya dace, kamar yadda kaakakin Yansandan jahar Kano, DSP Abdullahi Haruna ya bayyana.

A yan kwanakin nan ana yawan samun matsaloli da suka tasowa a tsakanin ma’aurata wanda hakan ke kai ga dayansu ga daukan mummunan mataki a kan abokin zamansa, idan za’a tuna har yanzu ba’a kawo karshen dambarwar data dabaibaye kokarin kashe mijinta da wata Amarya ta yi a Kano ba, wanda ta caka masa wuka a ciki yana barci.

Haka zalika wani magidanci a garin Mubi na jahar Adamawa ya yi ma matarsa yankan rago, sa’annan ya yanke wasu sassan jikinta da kayan cikinta, daga bisani kuma jefar da gawarta a gaban asibiti.

Bugu da kari a garin Kaduna ma an samu wata mata da ta yi kokarin kashe mijinta bayan ta watsa masa tafasashshen ruwan zafi yayin da zai tafi masallaci domin gabatar da sallar Asuba, sa’annan ta bi shi da wuka, wai don yana so zai kara aure.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel