Babbar Sallah: Mai Mala Buni ya raba ma zawarawa, marayu da tsofaffi abincin Sallah

Babbar Sallah: Mai Mala Buni ya raba ma zawarawa, marayu da tsofaffi abincin Sallah

Gwamnatin jahar Yobe ta kaddamar da rabon kayan abinci ga dubunnan mabukata dake jahar da suka hada da tsofaffi wanda karfinsu ya kare, zawara da mazajensu suka rasu, da kuma kanann yara marayu da suka rasa iyayensu.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito gwamnan jahar, Mai Mala Buni ne ya kaddamar da rabon a garin Buni Yadi, inda ya raba ma talakawa 5,000 kayan abinci daban daban, ya ce sun yi haka ne don taimaka ma mutanen da ba zasu iya zuwa gona don noma abinci ba ko su rike kansu ba.

KU KARANTA: Jami’ar kasar Sudan za ta bude tsangayar ilimin likitanci a jahar Zamfara

Babbar Sallah: Mai Mala Buni ya raba ma zawarawa, marayu da tsofaffi abincin Sallah
Babbar Sallah: Mai Mala Buni ya raba ma zawarawa, marayu da tsofaffi abincin Sallah
Asali: Facebook

Babban sakataren hukumar bada agajin gaggawa na jahar, Dakta Goje Muhamamd ne ya wakilci gwamnan a yayin rabon kayayyakin, inda yace wadanda suka amfana da wannan tagomashi yan gudun hijira ne da suka fara komawa garuruwansu a Buni Yadi, Buni Gari da Kukawa.

“Gwamna Mai Mala Buni ya umarceni na binciko tsofaffi daga cikin wadanda suka koma garuruwansu, mu dauki bayanansu, kuma dasu zamu fara a duk lokacin da irin wannan tallafin ya zo. Wadanda suka amfana da wannan tallafi zasu samu kilo 50 na shinkafa, alkama kilo 20, man gyada kilo 5, muna fata hakan zai basu abincin da zasu ci.” Inji shi.

Daga bisani Goje ya yi kira ga jama’an da kasa su sayar da kayan abincin, inda yace sun sanya matakan gano duk wanda ya yi kokarin sayar da kayan abincin da aka bashi, haka zalika ya yi kira ga kungiyoyi masu zaman kansu dasu taimaka ma yan gudun hijiran da suka koma garuruwansu.

Wata mata daga cikin wadanda suka amfana, Aisha, ta bayyana godiyarta ga hukumar SEMA bisa taimaka musu da ta yi da kayan abincin Sallah, sa’annan ta mika godiyarta ga gwamnan jahar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel