Gwmamnan jahar Bauchi ya sauke ma yan fansho naira miliyan 100

Gwmamnan jahar Bauchi ya sauke ma yan fansho naira miliyan 100

Gwamnan jahar Bauchi, Sanata Bala Muhammad ya bada umarnin biyan naira miliyan 100 a matsayin kudin giratuti ga yan fansho da suka yi ritaya daga aikin gwamnati a jahar Bauchi.

Shugaban ma’aikatan jahar, Nasiru Yelwa ne ya sanar da haka a ranar Talata a garin Bauchi, inda yace gwamnan ya bada umarnin sakar ma hukumomin fansho na gwamnatin jaha data kananan hukumomi naira miliyan hamsin hamsin.

KU KARANTA: Gwamna Abubakar ya shiga sahun musulmai masu gudanar da aikin Hajji a Saudiyya

Nasiru Yelwa ya kaddamar da raba kudaden a ranar Talata, 6 ga watan Agusta yayin da yake mika takardun kudi na Cheque ga wasu daga cikin tsofaffin ma’aikatan. Ya kara da cewa gwamnati ta saki kudin ne don biyan ma’aikatan da suka yi ritaya daga watan Agustan 2011 zuwa Oktoban 2011.

Yayin da ma’aikatan da suka yi ritaya a kananan hukumomi daga watan Oktoban 2010 zuwa Disambar 2010 ne kadai zasu samu wadannan kudade, sai dai yace za’a iya hadawa da ma’aikatan da suka yi ritaya a watan Janairun 2011.

Nasiru ya cigaba da cewa za’a bada fifiko ga iyalan tsofaffin ma’aikatan da suka mutu don rage musu radadin mawuyacin halin da suke ciki, sa’annan yace an fara aikin tantance yan fanshon tare da biyansu a cibiyoyi guda biyu dake jahar.

Daga karshe yace gwamnati zata cigaba da wannan tsari na biyan yan fansho hakkokinsu a duk wata domin ta rage tarin bashin dake kan gwamnatin jahar, sa’annan ya jinjina ma Gwamna Bala Muhamamd da ya cika alkawarin dauka.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng