Sallah: Buhun shinkafa ya koma N18,000 yayinda farashin kayan abinci yayi tashin gauron zai a Lokoja

Sallah: Buhun shinkafa ya koma N18,000 yayinda farashin kayan abinci yayi tashin gauron zai a Lokoja

Gabannin bikin babban sallah, farashin wasu kayayyakin abinci ya karu daga tsakanin kaso biyar zuwa 10 a wasu kasuwanni da ke Lokoja, jihar Kogi.

Wani wakilin kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN), da ya ziyarci kasuwanni a yau Talata, 6 ga watan Agusta ya bayyana cewa farashin shinkafa, wake, tumatir, man gyada, man ja da sauran kayan abinci sun tashi.

Binciken ya nuna cewa babban buhun shinkafa na 50kg da ake siyarwa kan N16,000 a baya ya tashi zuwa tsakanin N17,000 da N18,000 a kasuwanni.

A kasuwannin, ana siyar da kwanun shinkafa kan N600, wanda a makon da ya gabata ake siyar dashi kan N500.

Binciken ya kuma bayyana cewa farashin shinkafa yar gida na nan yadda yake N21,000 kowani buhu na 80kg.

KU KARANTA KUMA: Zanga-zangar juyin hali: An zuba manyan jami’an tsaro a sabon wajen taron na Lagas

Kwanun farin wake da ake siyarwa kan N350 ya tashi zuwa N500 yayinda buhun 10kg na Semovita ya koma N3,100 maimakon yadda yake a baya N2,900.

Wata yar kasuwa mai suna Misis Faith Audu, wacce ta zanta da NAN, ta bayyana cewa an samu hauhawan farashin kayayyakin abinci ne saboda bikin babban sallah mai zuwa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel