Tirkashi: Budurwa tayi ta surfawa saurayinta zagi kala-kala bayan ta gano cewa yana zuwa yayi lalata da kawarta

Tirkashi: Budurwa tayi ta surfawa saurayinta zagi kala-kala bayan ta gano cewa yana zuwa yayi lalata da kawarta

- Wata budurwa ta wallafa wani labarinta a shafin Twitter, inda ta dinga yiwa saurayinta zagi ta uwa ta uba bayan ta bankado wani sirri

- Budurwar ta gano cewa saurayinta yana cin amanarta da wata kawarta wacce suke makwabtaka da juna

- Budurwar ta gano labarin ne a shafin sada zumunta na Twitter yayin da wata ta saka

Wata budurwa mai amfani da shafin sada zumunta na Twitter ta wallafa wani labari na yadda ta gano cewa saurayinta yana cin amanarta da kawarta wacce suke makwabtaka da juna.

Ga abinda budurwar ta rubuta a shafin nata:

"Na ga lamarin naku yayi karfi har ya kawo zuwa shafin Twitter. Iyayenka sai sun tambayeka mai ka yiwa rayuwarka da yasa ka shiga halin da zan saka ka a ciki. Sannan ita kuma Lamy, dama can na san ke karuwa ce, amma ki cigaba."

KU KARANTA: Annabin karya da ya fito daga kasar Amurka ya mutu, kwanaki kadan bayan ya kai ziyara kasar Kenya

Budurwar ta gano hakan ne a shafin Twitter cewa saurayinta na zuwa ya kwanta da kawarta, inda ba ta yi kasa a guiwa ba ta dinga surfa masa zagi kala-kala.

Ga maganar da ta gani a shafin Twitter din wanda yasa ta yi wannan furuci akan saurayinta da kawarta:

"Idan sunanki Shade, kuma kina zaune a Magodo, to ki sani cewa saurayinki Chidi zai je gidan rawa da Lamy wacce take makwabciyarki, bayan haka kuma sun shirya yadda zasu kwanta idan sun gama holewa a gidan rawar."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel