An bi wani magidanci har gidansa an harbe shi a Katsina

An bi wani magidanci har gidansa an harbe shi a Katsina

Wasu 'yan bindiga da ba san ko su wanene ba sun halaka Alhaji Abdu Lawal da aka fi sani da Alili a gidan sa da ke unguwar Yammawa a cikin birnin Katsina.

'Yan bindigan sun kashe shi ne ta hanyar harbinsa da bindiga har sai da ya ce ga garin ku.

Alhaji Abdu Lawal babban direba ne a wani gidan mai da ke Kofar Guga kafin rasuwarsu.

Za a ayi jana'izarsa a unguwar Yammawa a ranar Talata bisa tsarin addinin musulunci.

Wannan na zuwa ne kwanaki kadan bayan gwamnonin jihohin Arewa maso Yamma sun yi afuwa ga 'Yan bindiga da masu garkuwa da mutane a jihohin arewa ciki har da jihar Katsina.

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Wata dalibar Jami'a ta kashe kanta saboda ta fadi jarrabawa

Gwamnonin sun yi wannan afuwar ne bayan taron neman kawo zaman lafiya da sulhu da aka yi a garin Katsina da ya samu hallarci jami'an tsaro, shugabanin 'yan bindiga.

Gwamna Aminu Masari na jihar Katsina ya ce gwamnonin Arewa maso Yamma sun yi wa 'yan bindiga da barayin shanu afuwa saboda yunkurin da ake yi na wanzar da zaman lafiya a yankin.

Masari ya bayyana hakan ne cikin rahoton bayan taro da aka karanta a karshen taron tsaro da sulhu na kwana guda da aka gudanar tare da jami'an tsaro, da 'yan kungiyar sa kai da makiyaya da manoma a ranar Alhamis a Katsina.

Sakamakon sulhun, an haramta ayyukan 'yan kungiyan sa-kai a jihohin na arewa maso yamma.

Gwamnonin arewan sun bukaci a kyalle makiyaya da iyalansu su cigaba da harkokinsu ba tare da tsangawa ba sannan an bukaci 'yan bindigan su ajiye makamansu kuma su dawo da dukkan dabobin da ke hannunsu tare da sakin mutanen da su kayi garkuwa da su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel