Gwamna Ganduje ya yi ma yan wasa ruwan daloli a jahar Kano

Gwamna Ganduje ya yi ma yan wasa ruwan daloli a jahar Kano

Gwamnan jahar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya raba ma yan kwallon kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars dala dubu daya daya kyauta sakamakon nasarar da suka samu wajen lashe kofin gasar Aiteo.

Legit.ng ta ruwaito dala 1000 daidai yake da kimanin naira N360,000, wanda Gandujen ya bayyansu a matsayin somin tabi duba da namijin kokarin da yan wasan suka nuna a wasan karshe na gasar Aiteo Cup da suka buga da kungiyar kwallo na Niger Tornadoes.

KU KARANTA: Karamar yarinya yar shekara 10 ta haihu a jahar Benuwe

Gwamna Ganduje ya yi ma yan wasa ruwan daloli a jahar Kano
Gwamna Ganduje ya yi ma yan wasa ruwan daloli a jahar Kano
Asali: Facebook

Wannan shine karo na daya da Pillars ta samu nasarar lashe gasar bayan shekaru 66, inda ta doke Niger Tornadoes da ci 4-3 a bugun daga kai sai gola bayan sun tashi wasa 0-0 a filin wasa na Ahmadu Bello dake garin Kaduna.

Kaakakin gwamnan, Abba Anwar ya bayyana cewa akwai sauran alherin da gwamnan zai yi ma yan wasan, ya kara da cewa gwamnatin za ta shirya ma yan wasan liyafar cin abincin dare nan bada jimawa ba.

“Mun raba muku wannan kudi ($1,000) ku 40 ne don bayyana godiyarmu gareku, kuma wannan kadan daga cikin alherin dake zuwa kenan nan bada jimawa ba. Kungiyar kwallon Kano Pillars ce mafi girma a Najeriya, kuma duk yan Najeriya sun san wannan.

Gwamna Ganduje ya yi ma yan wasa ruwan daloli a jahar Kano
Gwamna Ganduje ya yi ma yan wasa ruwan daloli a jahar Kano
Asali: Facebook

“Dolene mu bayyana farin ciki da murnarmu bayan mun samu nasara a kan Niger Tornadoes, yan wasanmu suna da ladabi da biyayya ga kishin kasa, muna alfahari da matasanmu, muna alfahari da Kano Pillars.” Inji shi.

A nasa jawabin, shugaban kungiyar Pillars, Suraj Shuabu Yahaya ya yaba ma kokarin da gwamnan jahar Kano ya yin a na ciyar da kungiyar gaba, ya kara da cewa zasu cigaba da tabbatar da ladabi a tsakanin yan wasan Kano Pillars.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel