Yanzu-yanzu: An harbe mataimakin shugaban kungiyar Miyetti Allah har lahira

Yanzu-yanzu: An harbe mataimakin shugaban kungiyar Miyetti Allah har lahira

An hallaka wani babban jigon shugaban kungiyar makiyayan Najeriya wadda aka fi sani da Miyetti Allah MACBAN.

An hallaka Marigayin, Saidu Kolaku, wanda ya kasance mataimakin shugaban kungiyar na Kudancin jihar Adamawa, ranar Asabar, 3 ga watan Agusta, 2019.

Wani jami'in kungiyar MIyetti Allah da sauran gama-garin jama'a sun bayyana cewa masu jin haushinsa ne suka kashehi saboda yana taimakawa jami'an tsaro wajen bibiyar masu garkuwa da yan baranda.

Kwanakin bayan nan hukumar yan sandan Najeriya suka karramashi sakamakon namijin kokarin da yakeyi.

KU KARANTA: Tsohon shugaban INEC, Attahiru Jega, ya shiga siyasa

Kakakin hukumar yan sandan jihar Adamawa, Sulaiman Nguroje, ya tabbatar da wannan labari.

YAce: " Wasu yan bindiga sun dira gidan shugaban yan Fulani dake Sabon Pegi, karamar hukumar Mayo Belwa, suka harbeshi."

"Bayan samun labarin jami'an yan sanda suka garzaya gidan kuma suka kaishi asibiti inda likita ya tabbatar da cewa ya mutu."

Ya kara da cewa kwamishanan yan sandan jihar ya tura jami'ai domin bincike kan wannan kisan gilla.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel