Shahararrun 'yan wasa 15 da ba su taba buga wa kasarsu ta haihuwa kwallo ba

Shahararrun 'yan wasa 15 da ba su taba buga wa kasarsu ta haihuwa kwallo ba

Akwai 'yan kwallon kafa da suka shahara sosai a duniya amma ba kasar su ta haihuwa suka buga wa tamallo ba.

Hakan na faruwa ne galibi ga 'yan kwallon da ke da izinin zama a kasashe biyu a lokacin guda hakan na tilasta su zaben kasa daya cikin biyun da za su rika buga wa kwallo.

'Yan kwallon na gabatar da dalilai daban-daban wurin zaben kasar da suke so su rika buga wa kwallo. Wasu daga cikinsu na da hujjoji masu karfi yayin da wasu dai akwai alamar tambaya kan zabinsu.

Ga dai jerin fitattun 'yan kwallon duniya 15 da ba su taba buga wa kasar su ta haihuwa kwallo ba.

1. Zinedine Zidane - Iyayensa Smail da Malika sunyi hijira daga kasar Algeria ne daf da yakin kasar na shekarar 1953 zuwa kasar Faransa.

Yana daya daga cikin fitattun 'yan kwallon Faransa saboda kwarersa da basirar sarrafa kwallon kafa. Zidane ya lashe kyaututuka masu yawa ciki har da dan kwallon duniya na FIFA sauku uku da Ballon D'Or.

2. Deco - Deco dan asalin kasar Brazil ne amma ya bar kasarsa ta haihuwa ya koma Portugal a 2003 ya buga wasansa ta farko da kasarsa ta haihuwa wato Brazil. Ya kuma buga wa kungiyoyin Porto, Barcelona da Chelsea kwallo.

DUBA WANNAN: An rufe gidan dan majalisar tarayya da aka gano kayan talakawa dankare a ciki

3. Clarence Seedorf - Kasarsa ta haihuwa ita ce Kamaru amma daga baya ya koma kasar Holland inda ya zama daya daga cikin fitattun 'yan kwallo da suka kafa tarihi a lokacin su. Ya fara buga wa Holland kwallo ne a 1994.

4. Lilian Thuram - Thuram haifafan garin Pointe-a-Pitre ne da ke kasar Guadeloupe amma a shekarar 1994 ya fara bugawa kasar Faransa kwallo. Yana daga cikin tawagar kwallon kafa na Faransa da suka lashe kofin duniya a 1998 da 2018.

5. Mauro Camoranesi - An haifi Camoranesi ne a garin Tandil da ke kasar Argentina amma ya koma buga wa kasar Italy kwallo saboda dama can asali kakansa daga Italy ya yi hijira ya tafi Argentina 1973.

6. Patrick Viera - Patrick Viera haifafan dan kasar Senegal ne amma ya koma Faransa tun yana shekara 8 da haihuwa. Ya fara buga wa Faransa kwallo ne a shekarar 1997.

7. Eusebio - Eusebio haifafan kasar Mozambique ne amma kasar Portugal ya ke buga wa kwallo. Ya fara buga kwallo a Portugal a shekarar 1961 kuma yana daya daga cikin wadanda aka alfahari da su saboda bajintarsa.

8. Nani - Nani haifafan dan kasar Cape Verde ne amma kuma Portugal ya buga wa kwallo. Ya fara buga kwallo a Portugal a shekarar 2006.

9. Gonzalo Higuain: An haife shi a garin Brest da ke Faransa kuma ya fara buga a Faransa kamar mahaifinsa amma daga bisani ya nemi izinin zama dan kasar Argentina kuma aka bashi. Ya fara buga wa Argentina kwallo a 2007.

Sauran 'yan wasan da suka hada da Pepe, Lukas Podolski, Edgar Davids, Eduardo, Jimmy Floyd Hasselbaink da John Barnes.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel