Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un: Tsananin talauci yasa mutanen kasar Haiti suna cin tuwon kasa don su samu su rayu

Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un: Tsananin talauci yasa mutanen kasar Haiti suna cin tuwon kasa don su samu su rayu

- Kasar Haiti tana daya daga cikin kasashen da suke fama da tsananin talauci da yasa har suke cin kasa a matsayin abinci

-A kasar Haiti, mafi yawan mutanen kasar suna dogaro da kasa da kuma dalar Amurka 2 don rayuwa a rana

So da yawa iyaye kan nunawa yara muhimmancin cinye abinci idan suka fara ci, ba tare da an bar ragowa ko an wulakanta shi ba. Sukan fada musu cewa akwai wasu sassa a duniya ma da yara ke faduwa su mutu saboda bakar yunwa. Wannan ba barazana bace kawai, gaskiya ce kuma yana faruwa.

Kamar yanda kungiyar abinci da noma da kiwo ta majalisar dinkin duniya ta fada, akalla ana wulakanta ton biliyan 1.3 na abinci da za'a iya ci, inda hakan ke kawo lalacewar tattalin arziki na kusan dalar Amurka miliyan 750 a duk shekara. Da tsananin yunwa da wasu kasashen ke fuskanta, barin abinci ya lalace babban almubazzaranci ne.

KU KARANTA: Na gida basu koshi ba za a kaiwa na dawa: Ka taimaka ka kawo karshen rikicin dake faruwa a kasata - Firaministan Libya ya roki Buhari

Bari muyi misali da kasar Haiti.

A kasar da mafi yawan mutane na rayuwa a kasa da dalar Amurka 2 a kullum. Samun kayan marmari da sauran kayan abinci tamkar mafarki ne. Babu kudin siyan kayan abinci masu gina jiki. A don haka ne suka dogara akan lakka ko kuma jar kasa don samun su rayu.

Bayan gini da akeyi da jar kasar, mutanen kasar Haiti suna cin kasar. Masana sun tabbatar da cewa tana da illa ga lafiyar jikin Dan adam. Bayan yiwuwar samun kwayoyin cututtuka dake cikin kasar, mutanen dake dogaro akan cin jar kasar don rayuwa na da yiwuwar kamuwa da cutukan rashin ingantaccen abinci.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng