An yiwa wata budurwa bulala 100 a bainar jama'a bayan an kama ta da laifin aikata zina da wani saurayinta

An yiwa wata budurwa bulala 100 a bainar jama'a bayan an kama ta da laifin aikata zina da wani saurayinta

- An yiwa mutane uku bulala a bainar jama'a a kasar Indonisiya

- Ciki hadda masu aure, wadanda suke da shekaru 22, an yi musu bulala dari-dari bayan an kama su da laifin aikata zina

- Haka kuma an yiwa wani saurayi dan shekara 19 bulala shima bayan kama shi da laifin zina

Wata mata ta koka inda ta bukaci wani mutumi da yake yi mata bulala da ya daina dukanta, a lokacin da ake yiwa masu laifi irin nata bulala ranar Larabar nan da taa gabata a kasar Indonisiya.

Matar mai shekaru 22, wacce aka yi mata hukunci akan laifin da ta yi na zina, tana daya daga cikin mutane ukun da aka yiwa bulala dari a ranar.

Mutane masu dumbin yawa suna kallo a lokacin da ake yiwa mazan guda biyu da mace daya bulala a filin wasa na Lhokseumawe,.

KU KARANTA: Ba sani ba sabo: An dakatar da shugaban karamar hukuma da Hakimi a jihar Zamfara

Bulala ana yinta ne a matsayin hukunci ga wasu laifuka da suka hada da caca, shan giya, luwadi da kuma zina ba tare da aure ba a yankin tsibirin SUmatra.

Ranar Larabar budurwar da saurayinta an yi musu bulala dari-dari, inda budurwar ta ta dinga faduwa saboda zafin bulalar.

Haka shima wani saurayi dan shekara 19 wanda aka kama shi da laifin zina, an yi masa bulalar inda har rigar shi ta jike da jini.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng