Majalisar Musulunci ta koli yi karin haske game da ganin watan Zulhijja

Majalisar Musulunci ta koli yi karin haske game da ganin watan Zulhijja

Kwamitin ganin wata na majalisar koli ta Musulunci a Najeriya, NSCIA, ta sanar da cewa bata samu rahoton ganin watan Zulhijja daga ko ina a Najeriya ba a ranar Alhamis, 1 ga watan Agusta.

Tun a ranar Laraba ne, 31 ga watan Agusta, wanda yayi daidai da 28 ga watan Zulkida mai alfarma sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar ya yi kira ga al’ummar Musulmai dasu fita neman jinjirin watan Zulhijja na shekarar 1440.

KU KARANTA: Sulhu: Masu garkuwa da mutane sun sako wani hakimi da iyalansa a jahar Zamfara

Akwai matakai da ake bi wajen tabbatar da ganin watan Musulunci a Najeriya, shine, idan wani mutum ko wasu mutane sun gani, zasu sanar shuwagabannin gargajiya na yankin, kamarsu dakaci, ko hakimi, wanda zasu isar da sakon ga Sarki, shi kuma Sarki ya isar da sakon ga fadar mai martaba Sarkin Musulmi.

Idan har kwamitin ganin wata ta tabbatar da ganin shikenan sai mai alfarma Sarki ya sanar da ganin wata, wanda hakan ke kawo karshen tsohon wata da shiga sabuwar watan Musulunci, amma a inda kwamitin bata ga watan ba, sai a turata garin da aka ce wani ko wasu sun gani domin su bincika su tabbatar, daga nan sai a dauki matakin daya kamata.

Sai dai da safiyar Juma’a, 2 ga watan Agusta ne kwamitin ganin wata ta sanar a shafinta na kafar sadarwar zamani ta Facebook, inda tace bata samu rahoton ganin watan ba, don haka bisa amfani da ganin watan Zulhijja a kasar Saudiyya, majalisar Sarkin Musulmi ta sanar da Juma’a, 2 ga watan Agusta a matsayin 1 ga watan Zulhijja.

Kwamitin ta bayyana cewa sarkin ya dauki matakin ne bayan tattaunawa tare da musayar ra’ayi da manyan malaman musulunci, kamar yadda ya saba yi a duk lokacin da bukatar hakan ta taso.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel