An samu rabuwar kai a tsakanin mabiya Zakzaky

An samu rabuwar kai a tsakanin mabiya Zakzaky

Hasashen jama’a sun nuna cewa an samu rabuwar kai a tsakanin mabiya mazhabar Shi’a karkashin jagorancin Sheikh Ibrahim El-Zakzaky.

Hakan ya biyo bayan banbancin ra’ayin da aka samu daga bangarorin mambobin kungiyar ta IMN, akan batun janye zanga-zangar neman a saki shugabansu wanda ke tsare a hannun hukuma tun a shekarar 2015.

A ranar Laraba, 31 ga watan Yuli ne dai mai magana da yawun kungiyar Islamic IMN, Ibrahim Musa ya bayar da sanarwar cewa sun dakatar da zanga-zangar su ta wani lokaci saboda wasu sabbin cigaba da aka samu.

Sai dai kuma a bangare guda Jagoran zanga-zangar, Malam Sunusi Abdulkadir ya ce babu ruwansu da wadanda suka ce wai su sun dakatar da zanga-zanga zuwa wani lokaci inda ya ce su addini su ke yi ba siyasa ba.

Ya kuma jadadda cewa ba za su taba dakatar da zanga-zanga ba har sai lokacin da aka sako Sheikh Zakzaky.

KU KARANTA KUMA: Suhaila Zakzaky ta bayyana cewa yan Shi’a zasu cigaba da zanga zanga a kan tituna

Hakazalilka wata da ke ikirarin cewa 'ya ce ga jagoran mabiya kungiyar mai suna Suhaila Ibrahim Elzakzaky ta bukaci mutanensu da su ci gaba da zanga-zargar da suke yi ta neman a sake jagoran nasu.

Wannan dalilin ne yasa wasu ke ganin cewa wannan karon da suke yi da juna a kan matsayinsu, wata alama ce da ke nuna cewa an samu baraka a tsakanin magoya bayan `yan kungiyar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel