'Yan bindiga sun kai farmaki kauyuka hudu a Katsina

'Yan bindiga sun kai farmaki kauyuka hudu a Katsina

'Yan bindiga dauke da muggan makamai sun kai hari a kauyukan Wagini, Shekawa, Chambala da 'Yar Laraba a karamar hukumar Kankara na jihar Katsina.

Wata majiya ta ce 'yan bindigan sun kwashe kimanin awanni biyu suna cin karen su ba babbaka kafin jami'an tsaro suka fatattake su.

Mazauna kauyukan sun ce an raunata wani dan kungiyar sa kai da wasu mazauna garin biyu Nafiu Danwanzam da Hamisu Wagina yayin harin.

DUBA WANNAN: Saurayi ya kashe ya budurwarsa bayan ta raina kwazonsa a gado

Sun kuma ce an kone motoccin sojoji guda uku.

"Harin ya sanya mutane da dama kaura zuwa garin Batsari da ke ganin kaman nan ne ya aka fi samun tsaro.

"Kawo yanzu, ba za mu iya tabbatar da adadin mutanen da suka rasu ko suka yi rauni ba a bangaren 'yan bindigan da suka iso kauyen kan babura masu yawa suna ta harbe-harben bindiga," a cewar majiyar.

A wani rahoton. Legit.ng ta kawo muku cewa shugaba Muhammadu Buhari ya ce gwamnatisa za ta fara aiwatar da wasu dabarun kawo karshen kallubalen tsaro da ake fama da shi a kasar.

Shugaba Buhari ya ce gwamnatinsa za ta saka na'urorin daukan hoton bidiyo a manyan tituna da muhimman wurare tare da daukan sabbin jami'an tsaro da za a tura su aiki a kananan hukumominsu da kuma cigaba da yin hadin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel