Dan Osama bin Laden, Hamza ya rasu - Rahoton Amurka

Dan Osama bin Laden, Hamza ya rasu - Rahoton Amurka

Allah ya yi wa Hamza Bin Laden dan tsohon shugaban kungiyar 'yan ta'adda na al-Qaeda Osama bin Laden rasuwa.

Wani sabon rahoto da hukumomin tattara bayanan sirri na Amurka suka wallafa ya bayyana cewa dan tsohon jagoran na al-Qaeda ya rasu amma ba a bayar da cikakken bayanin sanadiyar rasuwarsa ba ko kuma kasar Amurka na da hannu cikin lamarin kuma shugaba Donald Trump na Amurka ya ki cewa komi kan lamarin.

"Ba zan ce komi a kan batun ba. Bana son in yi tsokaci a kan lamarin," a cewar Trump.

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Jam'iyyar APC ta dakatar da Abdulmumini Jibrin, ta fadi dalili

Tun a shekarar 2018 ne kungiyar al Qaeda ta fitar da wani bayanni da Hamza bin Laden ya yi inda ya yi wa Amurka barazana tare da kira ga mutanen yankin Larabawa su yi wa shugabanin su bore.

Sojojin Amurka ne suka kashe Osama bin Laden a shekarar 2011 yayin wani sumame da suka kai a mabuyarsa da ke Abbottabad a Pakistan.

Ba a tarar da Hamza a gidan ba sai dai an gano wasu wasiku da ke nuna cewa shugaban na al Qaeda yana son dan sa ya zo gidansa na Abbottabad domin ya bashi horo ya gaje shi a matsayin shugaban kungiyar.

"Ana bawa Hamza horo domin ya zama shugaba a kungiyar da mahaifinsa ya kafa" kuma akwai "yiwuwar zai samu goyon bayan daga shugabanin kungiyar. Duba da cewa kungiyar ta na dab da rushewa, Hamza ne mutum da ya fi dacewa da zama shugaban domin ya hada kan masu ikirarin jihadin," a cewar wani kwararre kan yaki da ta'adanci kuma tsohon ma'aikacin FBI, Ali Soufan a shekarar 2017.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel