Kasashen duniya 30 da suka yi kaurin suna wajen cin hanci
A ranar Talata ne wata kungiya da ke nazarin tattalin arzikin kasashen duniya (WEF) ta fitar da wani rahoto da ta saba fitar wa duk shekara a kan cin hanci.
Kungiyar ta yi amfani da alkaluma na ilimin tattalin arziki da gudanar da gwamnati wajen fitar da kasashen duniya 140 da suka yi kaurin suna wajen cin hanci da rasha wa. Sun yi hakan ne ta hanyar bayar da maki ga kowacce kasa daga 1 zuwa 100.
Idan kasa ta samu maki 100 a sikelin auna cin hanci, hakan na nufin babu cin hanci a wannan kasa kenan, idan kuma, alal misali, kasa ta samu sifili (zero) a matsayin makin ta, hakan na nufin ta na cikin sahun farko na kasashe da ke fuskantar matsalar cin hanci.
Dukkan kasashen da ke cikin wannan rahoto sun sami makin da ya gaza kai wa 30.
Ga jerin Kasashen;
1. Sierra Leone
2. Iran
3. Gambia
4. Rasha
5. Paraguay
6. Mexico
7. Bangladesh
8. Mauritania
9. Lebanon
10. Kenya
DUBA WANNAN: 'Yan Afrika birai ne da har yanzu basu saba da saka takalmi ba - Tsohon shugaban kasar Amurka
11. Guinea
12. Najeriya
13. Uganda
14. Cameroon
15. Mozambique
16. Haiti
17. Burundi
18. Zimbabwe
19. DR Congo
20. Cambodia
21. Chad
22. Angola
23. Venezuela
24. Yemen
25. Ukraine
26. Mexico
27. Kyrgyzstan
28. Guatamela
29. Honduras
30. Laos
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng