Tsaro: Gwamnatin Zamfara ta dakatar da shugaban karamar hukuma da Hakimi

Tsaro: Gwamnatin Zamfara ta dakatar da shugaban karamar hukuma da Hakimi

Majalisar dokokin jihar Zamfara ta dakatar da shugaban karamar hukumar Maradun, Alhaji Ahmad Abubakar, bisa zarginsa da saba wa umarnin gwamnati a kan harkokin da suka shafi tsaro a jihar.

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya bayyana cewa gwamna Bello Matawalle ya bullo da tsarin tattauna wa domin yin sulhu da 'yan bindiga a kokarinsa na dawo zaman lafiya jihar Zamfara.

Kazalika, gwamnan ya hana kisan Fulani da 'yan bindiga ko kai musu hari a duk inda aka gansu a fadin jihar Zamfara.

Shugaban majalisar dokokin jihar Zamfara, Alhaji Nasiru Magarya, ne ya sanar da dakatar da shugaban karamar hukumar yayin zaman majalisar na ranar Talata bayan majalisar ta karbi korafi a kansa da wasu masu kishin karamar hukumar suka mika ga majalisar.

NAN ta rawaito cewa korafin da majalisar ta karba na dauke da sa hannun Bello Abdullahi na mazabar Tsibiri, Amiru Sa'idu na mazabar Kaya, Musa Muhammad na mazabar Damaga/Gamagiwa, Mu'awiya Sardauna na mazabar Faru, M. Sulaiman na mazabar Gora da Bashiru Saleh na mazabar Gidangoga.

DUBA WANNAN: 'Yan Afrika birai ne, har yanzu basu saba da saka takalmi ba - Tsohon shugaban kasar Amurka

Masu korafin sun zargi shugaban karamar hukumar da nuna halin rashin kula wa ga kokarin gwamnatin na samar da zaman lafiya ta hanyar kin sauke da ke wuyansa a matsayinsa na babban jami'in tsaron karamar hukumar.

Da yake karanta takardar korafin bisa umarnin shugaban majalisar, magatakardan majalisar, Alhaji Abdullahi Bayaro, ya bayyana cewa shugaban karamar hukumar ya hada kai da wasu 'Yansakai tare da korar Fulani makiyaya daga yankin karamar hukumar Maradun, lamarin da ya saba da umarnin da gwamnatin jihar ta bayar.

Da ya ke tofa albarkacin bakinsa a kan lamarin, Alhaji Faruk Dosara, dan majalisa mai wakilatar mazabar Maradun, ya ce majalisar ta karbi korafe-korafe da dama a kan shugaban karamar hukumar.

Kazalika, majalisar ta dakatar da Alhaji Abubakar Rafi, hakimin Boko ta Yamma a masarautar Moriki da ke karamar hukumar Zurmi.

Majalisar ta dakatar da Basaraken ne bayan kwamitin binciken da aka kafa a kansa ya same shi da laifin kwace gonakin jama'a, kamar yadda jama'arsa suka shigar da korafi a gaban majalisar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel