Saurayi ya kashe ya budurwarsa bayan ta raina kwazonsa a gado

Saurayi ya kashe ya budurwarsa bayan ta raina kwazonsa a gado

Wani kwarare a fanin sadarwa da shekara 33, Maxim Gareyev ha amsa cewa shine ya kashe masoyiyarsa, marubuciyar salon kwalliya, Ekaterina Semochkina 'yar shekaru 24 kuma saka gawarta cikin jaka.

Ya ce Semochkina ta yi masa gori cewa ba shi da kwazo wurin kwanciyar masoya kuma ta ce masa talaka.

A cewar jaridar Daily Mail, Gareyev ya shaidawa 'Yan sandan kasar Rasha cewa ya kashe ta ne bayan sun hadu domin saduwa.

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: 'Yan Shi'a sun dakatar da zanga-zanga, sun bayyana dalilansu

Ya ce, "Ta yi ta zagi na sosai. Ta rika zagi ne cewar bani da bajinta wurin saduwa kuma bani da kudi. Abin ya min ciwo sosai na kasa jure wulakancin da cin fuskan.

"Na caka mata wuka a kalla sau biyar a wuyan ta da kuma kirjin ta."

Iyayen Semochkina sun gano gawarta ne da alamun yanka a wuyanta da kuma wasu raunuka a kirjin ta.

An tsinci gawar ta sanye da wani nauyin tufafi mai hade da safa da ake kira 'suspender belt' a gidan da ta ke haya a birnin Moscow.

Da aka tambaye shi ko ya yi nadaman abinda ya aikata, Gareyev ya ce, "Eh, nayi nadama kuma zan bawa jami'an tsaro hadin kai yayin gudanar da bincikensu."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel