Tirkashi: Rikici ya barke bayan Uwargida ta dawo daga Makkah ta tarar mijinta ya Auri mai aikinta

Tirkashi: Rikici ya barke bayan Uwargida ta dawo daga Makkah ta tarar mijinta ya Auri mai aikinta

- A wata hira da aka sanya a shafin yanar gizo na Youtube, ta nuna yadda wata mata take bambamin fada akan karin auren da mijinta yayi

- Matar wacce ake kyautata zaton mijin nata ya auri mai aikinta bayan ta tafi kasar Saudiyya aikin hajji, ta dawo ta nemi dole sai mijin ya saki amaryar ta sa

Ga dai yadda lamarin ya kasance, bayan an fara tuntubar uwargidan don jin ta bakinta.

"Wallahi dole sai ya sake ta, dan kaniyarsa dole kuma ya zauna dani, tunda shi ba ubana bane, kuma wallahi shi ba dan halak bane, inda dan halak ne shi babu yadda za ayi na tafi bautar ubangijina ba na dawo na tarar ya auri 'yar aiki na.

"'Ya'yanmu shida ni da shi, maza uku mata uku, abin bakin cikin ma yarinya yaje ya auro mini, idan shi yana fama da kuruciya ni na san inda yake yi mini ciwo."

KU KARANTA: Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un: Wani mutumi ya kashe mahaifiyarsa mai shekaru 81 saboda kawai ta yi korafi akan matarsa

To sai dai kuma da aka yi magana da mijin ta wayar salula ya bayyana lamarin yake:

"Ni wallahi Hajiya ba ta dauke a matsayin mijinta ba, ta dauke a matsayin dan aikine, wanda duk wata matsalarta ni take nema, banga amfanin ka auri mata koda yaushe ace tana hanya ba, daga Maiduguri, sai Kano, sai Legas shine kawai aikinta, in takaita muku zance Dubai ma sai taje sau hudu a shekara.

"Ni fah kamar bani da mata ne ma duka, sai yanzu dana sake yin aure na gane cewa ina da gata, kuma wallahi inda badan Malam ya kirani yayi mini nasiha ba da wallahi tuni na saketa."

Haka ita ma amaryar da aka tuntubeta ga abinda ta ce:

"Fiye da shekara goma Hajiya ita ce ta dauko ni daga kauye ina yi mata aiki a gidanta, muna zaune a haka sai mijinta ya nuna yana sona, ni kuma nake dan kaucewa saboda bana son matsala, da ya takura shine na amince bayan malamai sun nuna cewa hakan ba laifi bane.

"Daga baya iyaye suka sanya baki a maganar, lokacin idan tayi tafiyar ta sai ta jima bata dawo ba, kawai sai muka yi auren mu."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel