Allah daya gari bambam: Labarin wani gari da Maza da Mata ke magana cikin harshe daban daban

Allah daya gari bambam: Labarin wani gari da Maza da Mata ke magana cikin harshe daban daban

Lallai Allah daya gari bambam kamar yadda masu iya magana ke fada, an binciko wani gari dake jahar Cross Rivers a Najeriya inda al’ummar garin suke da wata baiwa, yadda Maza ke magana cikin harshe daban, mata ma suke magana cikin harshe na daban.

Sunan wannan gari Ubang, kuma yana nan ne a cikin karamar hukumar Obudu dake jahar, kuma hakan yasa jama’a da dama masu yawon bude suna tururuwa zuwa wannan gari don gane ma idanuwansu wannan abin al’ajabi.

KU KARANTA: Yan bindiga sun bindige hamshakin dan kasuwa, sun yi awon gaba da surukarsa

Daga garin Ubang zuwa birnin jahar Cross Rivers, watau Calabar, nisan tafiyan sa’o’I 6 ne, garin Ubang na zagaye ne da manyan dutwasu da suke baiwa garin kariya, yawancin jama’an garin manoman rogo da doya ne.

A cewar jama’an garin, dukkaninsu haka suka tashi suka tarar da wannan abin mamaki na yare biyu ga jinsi daban daban, don haka suka bayyana hakan a matsayin wata baiwa da Allah ya yi musu, kuma babban laifi ne a ji namiji na yin yaren mata, ko mace ta yi yaren maza.

Sai dai kowanni jinsi kuma yana fahimtar yaren dayan jinsin, kuma har yanzu haka ake zama a wannan gari, garin da a yanzu haka ya zama wata matattarar masu yawon bude da kuma manyan malaman ilimin harsuna da binciken tarihin halittar dan adam.

Bugu da kari a karamar hukumar Obudu akwai wani katafaren wajen kiwon shanu da ake kira Obudu Cattle Ranch wanda aka samar dashi tun a shekarar 1962, kuma tsohon gwamnan jahar… ya gyarashi tare da mayar dashi wajen shakatawa, hutawa da kuma yawon hude ido.

Wannan wuri an ginashi ne a saman tsauni, kuma yana daya daga cikin wuraren da kankarar dusa ke sauka a Najeriya saboda tsananin kyawun yanayin wajen.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel