Yan bindiga sun bindige hamshakin dan kasuwa, sun yi awon gaba da surukarsa

Yan bindiga sun bindige hamshakin dan kasuwa, sun yi awon gaba da surukarsa

Wasu miyagu yan bindiga sun kai mummunar farmaki gidan wani hamshakin dan kasuwa, AlhajiYusuf Garkar-Bore, inda suka kasheshi, sa’annan suka yi awon gaba da matar dansa, Aisha Yusuf, a jahar Kebbi.

Rahoton kamfanin dillancin labaru Najeriya, NAN, ta ruwaito wani daga cikin iyalan mamacin daya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa yan bindigan sun kashe Alhajin ne a gidansa dake garin Gulma cikin garin Kebbi da misalin karfe 2 na daren Lahadi.

KU KARANTA: An tseratar da Ganduje da mataimakan gwamnoni 3 yayin da rikici ya kaure filin wasa a Kaduna

Majiyar Legit.ng ta ruwaitoshi yana cewa: “A kirji suka harbu Alhaji sau da dama, mun yi gaggawar garzayawa dashi zuwa babban asibitin garin Argungu, amma a can suka tabbatar mana da cewa tuni Alhaji ya mutu, mun yi masa jana’iza kamar yadda musulunci ya tanadar.

“Kuma har yanzu bamu samu wani labari game da halin da matar dan Alhajin take ciki ba, sakamakon yan bindigan basu tuntubemu ba har yanzu.” Inji shi.

Shima kaakakin Yansandan jahar Kebbi, DSP Nafiu Abubakar ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda yace sun aika da jami’ansu zuwa inda lamarin ya auku, sai dai miyagun mutanen da suka tafka wannan ta’asa basu tuntubi kowa ba, inji shi.

A wani labarin kuma, Sojojin Najeriya dake karkashin Operation Harbin Kunama III da Operation Sharan Daji sun samu nasarar tarwatsa gungun wasu yan bindiga a kauyen Yarsanta dake cikin karamar hukumar Kankara ta jahar Katsina inda suka yi babban kamu.

Sojojin sun kama yan bindiga dake kashe mutane suna satar shanu tare da garkuwa da mutane guda 16, daga ciki har da shugabansu, wani dan kabilar Ibo, Monday Chikwunka mai shekara 36, wanda kuma shine likitan yan bindigan dake dubasu idan an harbesu ko kuma basu da lafiya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng