Masha Allahu: Gwamnatin Jigawa za ta gina masallacin mata na N57m a Jami’ar Dutse

Masha Allahu: Gwamnatin Jigawa za ta gina masallacin mata na N57m a Jami’ar Dutse

-Gwamnatin Jihar Jigawa za ta ginawa mata masallaci a Jami'ar Tarayya da ke Dutse

-Kakakin Sakataren gwamnatin jihar ne ya bada wannan sanarwa inda ya ce miliyoyin kudi aka ware domin soma yin aikin

-Akwai kafanoni gudu uku na 'yan kwangila dake neman a basu damar yin ginin wannan masallaci yanzu haka

Gwamnatin Jihar Jigawa ta bayyana aniyarta na gina masallacin mata a Jami’ar Gwamnatin Tarayya dake Dutse wato FUD kan kudi miliyan N57.

Kakakin Sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Ismail Ibrahim ne ya bada wannan sanarwar ta hanyar wani zance da ya fitar a Dutse babban birnin jihar Jigawa.

KU KARANTA:Tantance ministoci: Aikinku yana yin kyau, fadar Shugaban kasa ta yabawa Majalisa

Zancen ya ce, Alhaji Muhammad Dagaceri wanda shi ne babban sakataren ofishin SSG ya jaddada batun ginin yayin da aka kaddamar da shirin fara yin aikin a Dutse ranar Alhamis.

Har ila yau, zancen ya fadi cewa ‘yan kwangila uku ne ke fafutukar samun kwangilar yin wannan aikin. Shugaban kula da ayyuka da bin diddigi na jihar, Nura Jibo ya tabbatar wa yan kwangilar cewa kwamitin da aka nada domin tantance ‘yan kwangila zai yi aiki tsakani da Allah.

Daya daga cikin shugabannin kamfanin kwangilar dake neman a ba shi wannan aiki, Alhaji Garba Ismail, a madadin kamfanin Modgan Investment Limited ya ba gwamnatin tabbacin yin aiki mai inganci da kuma nagarta. Kamfanin dillacin labaran Najeriya ne ya fitar da wannan labari.

A wani labarin kuwa, za ku ji cewa, Fadar Shugaban kasan Najeriya ta yabawa tsarin yadda tantance ministoci ke cigaba da gudana a Majalisar dattawa.

Maitamakawa Shugaban kasa kan lamuran da suka shafi majalisar dattawa, Ita Enang ne ya bada wannan labari inda ya ce, maganar da Shugaban majalisar ya fadi gaskiya ce ba a Najeriya kadai ake yin haka ba, sauran kasashen duniya ma nayin hakan.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel