Ciwon ciki da sauran alamomi 5 na cutar hanta

Ciwon ciki da sauran alamomi 5 na cutar hanta

A yau ce ranar cutar Hanta ta duniya wato World Hepatitis Day. An hori mutane masu nakasun lafiya a kan kada su yi watsi da alamomin cutar yayin da suka fara bayyana a jikin su.

Alamomin cutar hanta sun rabu kashi daban-daban daga kanana zuwa manya. Su kan bayyana a jikin dan Adam bayan wata daya zuwa watanni hudu da kamuwa da cutar. A wani sa'ilin su kan bayyana bayan mako biyu da kamuwa.

Da yawa daga cikin kwararrun lafiya da kuma likitoci sun yi gargadin cewa, alamomin ciwon hanta ba sa bayyana a kan jikin wadanda suka kamu da ita musamman kanana yara.

Ga jerin wasu alamomin na cutar hanta masu bayyana a jikin dan Adam da suka kamu da ita kamar haka:

1. Ciwon ko kuma kullewar cikin akai-akai.

2. Sauyawar launin fata zuwa doruwa.

3. Kadewar launin idanu zuwa doruwa.

4. Yawan jin kasala ko kuma gajiya tare da yanayi na zazzabi.

5. Kaikayi a wasu sassa na jiki.

6. Tashin zuciya da kuma amai.

7. Sauyawar launin fitsari da kuma bayan gida zuwa wani turarren launi da ba a saba gani ba.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel