Jarumta: Wani jami'in dan sanda ya kama Ba-Amurken da ya ci mutuncin dan Najeriya a filin jirgi

Jarumta: Wani jami'in dan sanda ya kama Ba-Amurken da ya ci mutuncin dan Najeriya a filin jirgi

A ranar Laraba ne jami'an rundunar 'yan sanda na filin tashi da saukar jirage na Murtala Muhammad da ke Legas suka kama wani dan kasar Amurka, Breedlove Shawn, mai shekaru 52, saboda dukan wani ma'aikacin filin jirgin.

Lamarin ya faru a harabar filin jirgin saman bayan Mister Shawn ya karya dokar ajiye motoci ta hanyar ajiye motarsa a inda doka ta hana.

A yayinda ake kokarin janye motar Ba Amurken ne saboda karya dokar da ya yi, sai ya fito daga cikin motar tare da marin daya daga cikin ma'aikatan cikin fushi, lamarin da ya ja hankalin mutane a filin jirgin, kafin daga bisani jami'an 'yan sandan Najeriya su kama Mista Shawn su tsare shi.

DUBA WANNAN: Wani soja ya kashe kansa a barikin sojojin Abuja, ya bar wasiyyar a tambayi matarsa dalili

Da ya ke magana da manema labarai, Alhaji Lamidi Falekulo, shugaban kamfanin kula da ajiye motoci a filin jirgin, ya tabbatar da faruwar lamarin tare da bayyana cewa babu wani mutum da ya fi karfin doka kuma doka zata yi aiki a kansa.

Kazalika, DPO na ofishin rudnunar 'yan sanda da ke filin jirgin sama na Legas, Danjuma Garba, ya tabbatar da kama Ba Amurken tare da bayyana cewa za a gurfanar da shi a gaban kotun majistare da ke Ikeja bisa tuhuma guda biyu da suka shafi cin zarafi da raunata jikin mutum.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel