Sai da Mata sannan shugabanni su ke samun nasara – Aisha Buhari

Sai da Mata sannan shugabanni su ke samun nasara – Aisha Buhari

Uwargidan Najeriya, Hajiya Aisha Muhammadu Buhari, ta bayyana cewa Mata su ne kirjin nasarar da masu mulki su ke samu. Aisha Buhari ta ce har shugabannin kasashe, sai da Mata su ke kai ga ci.

Mai dakin shugaban kasar na Najeriya, ta yi wannan jawabi ne a wajen wani taro da kungiyar WILAT ta Mata ta shirya a Garin Abuja. An yi wannan taro na bana ne a Ranar Juma’a, 26 ga Watan Yuli.

A taron da wannan kungiya na Mata da ke harkar tuki da safara a Najeriya su ka shirya, an yi magana ne a kan hadin kan Matan a wajen aiki domin kawo bunkasar tattalin arziki da kuma cigaba.

A jawabin mai dakin shugaban kasar, ta nuna cewa Mata ‘yanuwanta za su samu nasara a rayuwa muddin su ka rika dafawa juna tare da hadin-kai a tsakani. Paul Tallen ce ta wakilci Buhari a wajen taron.

A jawabin na Hajiya Aisha Buhari, wanda Pauline Tallen ta karanta a madadin ta, ta yi kira ga Mata su hada kai tare da taimakawa juna. Buhari ta kuma yabawa kokarin da wannan kungiya ta ke yi wa Mata.

KU KARANTA: Wasu 'Yan bindiga sun kai hari a babban ofishin Jam'iyyar APC

A cewar Mai dakin na shugaban kasa Muhammadu Buhari, Mata na taimakawa shugabanni wajen samun nasara. Buhari ta ce har shugabannin kasashe da ke mulki, su na samun gudumuwa daga ‘Ya ‘ya mata.

“Dole ya zama a na sa ran mace za ta zama wata a kasar nan. Maza su na samun galaba a kan mu idan kan mu bai hadu a wuri guda ba. Na jinjinawa kokarin da ku ke yi.” Inji Mai girma Aisha Buhari.

Matar shugaban kasar ta cigaba da cewa: “Kuma na yi alkawari zan taimaka maku a duk lokacin da ku ke neman duk wani taimako.” Kamar yadda Daily Trust ta rahoto a Ranar 27 ga Watan Yuli na 2019.

Wanda ta kafa wannan kungiya ta WILAT a Najeriya, Aisha Ali-Ibrahim, a na ta jawabin, ta bayyana cewa koyawa mata sana’a tare da karfafa masu da ba jarin kasuwanci ya na cikin muradinsu.

Sabuwar shugabar wannan kungiya ta yanzu a fadin kasar nan, Folake Soji-George, ta yi alkawarinza ta dage wajen ganin an cigaba da koyawa Mata hanyar samun abinci domin su dogara da kansu.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel