Hotuna: An hako gawar Sarki Namarudu da matarsa a kasar Iraqi, an same su sanye da gwala-gwalai na naira biliyan 12
- A kasar Iraqi an haka wani kabari inda aka iske gawar Sarki Namarudu da matarsa a cikin kabarin
- An ga wasu gwala-gwalai da lu'ulu'u a cikin kabarin wanda aka yi musu kudi kimanin dalar Amurka miliyan talatin da biyar
- Sarki Namarudu dai shine sarkin da ba a taba yin Sarki mai arzikinsa ba a tarihi.
An hako gawar Sarki Namarudu a wani yanki dake kasar Iraqi, gawar ta sa da ta matarsa an same su sanye da kaya na gwala-gwalai da lu'ulu'u wanda aka yi musu kudi kimanin dalar Amurka miliyan talatin biyar ($35m), inda kudin ya kai kimanin naira biliyan sha biyu a kudin Najeriya.

Asali: Facebook
KU KARANTA: Tirkashi: An gano wata mata tana shan fitsarin karenta, inda ta bayyana cewa yana maganin cutuka da dama
Sarki Namarudu dai shine Sarkin da yayi zamani da Annabi Ibrahim (AS), tarihi ya nuna cewa akwai lokacin da Namarudu ya sa bayinsa suka gina wani katon rami ya sanya aka kunna wuta mai karfin tsiya a cikin ramin, sannan ya sanya aka jefa Annabi Ibrahim cikin wutar.

Asali: Facebook
Sai dai wani ikon Allah shine, wutar ba ta yi masa komai ba, saboda kiyayewar da Allah yake bai wa Annabinsa.
Sarki Namarudu dai shine sarkin da ba a taba yin Sarki mai arzikinsa ba a tarihi.

Asali: Facebook
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng