Tashin hankali: Dan wasan Arsenal, Mesut Ozil ya sha da kyar, bayan wani hari da 'yan fashi suka kai masa zasu kashe shi
- An kai wa fitattun 'yan wasan kwallon kafa na kungiyar Arsenal, Mesut Ozil da Kolasinac hari a yayin da suke tafiya
- An gano cewa mutanen da suka kai wa 'yan wasan hari, 'yan fashi da makami ne, inda suka bi 'yan wasan dauke da wukake
- An bayyana cewa dakyar 'yan wasan suka tsira da ransu sanadiyyar harin da 'yan fashin suka kai musu
Fitaccen dan wasan kwallon kafa na kulob din Arsenal, Mesut Ozil da Kolasinac sun ranta ana kare don neman mafaka bayan an wasu mutane da ake tunanin 'yan fashi ne sun kai musu hari da wukake, ranar Alhamis 25 ga watan Yuli.
Da take tabbatar da kai harin akan 'yan wasan, kungiyar kwallon kafar ta Arsenal ta bayyana cewa:
"Mun tuntubi 'yan wasan namu kuma duk sun tabbatar mana da cewa lafiyarsu lau."
KU KARANTA: Masu gari: 'Yar gidan Gwamna Ganduje ta gwangwaje Ado Gwanja da kyautar tsaleliyar mota
Mai magana da yawun hukumar 'yan sanda ya bayyana cewa 'yan fashi da makami ne suka kai wa 'yan wasan hari.
Ga abinda ya ce:
"Mun samu rahoton cewa wasu mutane akan babura sun yi yunkurin yiwa wani mutumi da yake tafiya a mota fashi.
"Direban da mutanen cikin motar sun samu sun sha dakyar, inda suka gudu zuwa wani wajen sayar da abinci dake Golders Green, ana suka samu suka yi magana da jami'in mu."
Har ya zuwa yanzu bamu kama kowa ba a cikin mutanen da ake zargin.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng