Tashin hankali: Kowanne dare sai aljani ya zo ya sadu dani ta baki - Wata mata ta kai kuka wajen Fasto

Tashin hankali: Kowanne dare sai aljani ya zo ya sadu dani ta baki - Wata mata ta kai kuka wajen Fasto

- Wata mata ta shiga wata coci ta roki babban faston cocin da ya taimaka mata ya cire mata wani aljani da yake zuwa mata cikin dare

- Matar wacce aka nuno ta a wani bidiyo tana kuka tana rokon faston ta bayyana cewa karo na biyu kenan da aljanin ya zo mata kuma duk zuwan da yayi sai ya sadu da ita

- Ta bayyana cewa ya zo ya sadu da ita ta baki da farko daga baya kuma yazo ya kwanta da ita, kuma tun daga lokacin har zuwa yanzu gabanta ciwo yake mata

Wani bidiyo da yake ta yawo a kafafen sada zumunta na zamani ya nuna yadda wani Fasto na wata coci da ba a bayyana sunanta ba yake cirewa wata mata aljani wanda ta bayyana cewa yana saduwa da ita kuma yana sanya mazakutarsa a cikin bakinta.

A bidiyon an jiyo muryar matar tana bayanin cewa lamarin ya samo asaline bayan aljanin ya zo wajenta ya sanya mazakutarsa a bakinta.

KU KARANTA: Tirkashi: Ko masinja bai kamata shugaba Buhari ya bawa Nanono ba, balle minista - Dan Bilki Kwamanda

Ta cigaba da cewa daga baya kuma aljanin ya sake dawowa a karo na biyu domin ya sadu da ita ta hanyar kwanciya da ita, kuma tun daga lokacin take jin gabanta yana yi mata kaikayi.

Sai dai kuma a irin wannan yanayin ne Fastoci da yawa suke yin amfani da damarsu wajen neman mata masu irin wannan larura suyi zina dasu.

An sha kama shugabannin addini kala-kala da laifuka da yawa da suka shafi zina, fyade luwadi da sauransu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel