Da duminsa: Kauran Bauchi ya yi sabuwar amarya balarabiya

Da duminsa: Kauran Bauchi ya yi sabuwar amarya balarabiya

Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya auno sabuwar amarya balarabiyar kasar Labnan amma mazauniyar Najeriya.

Wannan labarin ya bayyana ne ranar Juma'a inda mai magana da yawun gwamnan, Ladan Salihu, ya ce an daura wannan aure a Masallacin Syriya dake Jihar Legas.

Sabuwar amaryar za ta kasance matar gwamnan ta biyu.

Kauran Bauchi ne gwamnan Najeriya na uku wanda ya kara aure jim kadan bayan darewa karagar mulki. Ya bi sahun gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni da gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, wanda ya yi aure bayan zabe.

Yace: "Alhamdulillah yau min shaida Fatihar Amaryar Gwamnan Jihar Bauchi Sen Bala A Muhammad a Masallachin Syria dake Ribadu Road a Lagos. Allah ya bada zaman lafiya. Amin."

Kalli hotunan:

Da duminsa: Kauran Bauchi ya yi sabuwar amarya balarabiya
Limaman Masallacin
Asali: Facebook

KU KARANTA: Babu wani rikici tsakanin Jibrin da Gbajabiamila - Yan majalisa

Da duminsa: Kauran Bauchi ya yi sabuwar amarya balarabiya
Kauran Bauchi ya yi sabuwar amarya balarabiya
Asali: Facebook

Da duminsa: Kauran Bauchi ya yi sabuwar amarya balarabiya
Da duminsa: Kauran Bauchi ya yi sabuwar amarya balarabiya
Asali: Facebook

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel