Assha: An damke wani mai gadin coci da ya bi dare ya sace kudin baiko

Assha: An damke wani mai gadin coci da ya bi dare ya sace kudin baiko

Wana mai gadi mai shekeru 20, Micheal Nwaogwu ya gurfana gaban kotun Majistare da ke zaman ta a Yaba a Legas a ranar Juma'a bisa tuhumarsa da ake yi na sace N2,385 daga akwatin tara kudin sadaka na coci da ake kira baiko.

Rundunar 'Yan sanda na tuhumar Nwaogwu, mazaunin unguwar Costain da ke Legas da laifin sata.

Sai dai ya ce shi bai aikata laifin da ake zarginsa ba.

Dan sanda mai shigar da kara, Saja Godwin Oriabure ya shaidawa kotu cewa wanda aka gurfanar ya aikata laifin ne a tsakar daren ranar 17 ga watan Yuli a Cocin Katolila ta St. Dennis da ke Akoka Bariga a Legas.

DUBA WANNAN: El-Zakzaky: Sheikh Ahmad ya fadawa gwamnati yadda za a magance matsalar 'yan shi'a

Oriabure ya yi ikirarin cewa wani mai gadin mai suna Mista Musa Ayay ne ya gano cewa an balle akwatin sadakar.

Ya ce wanda aka yi karar ya amsa cewa shi ya aikata laifin a lokacin da Ayay ya tambaye shi.

Ayay ya yi ikirarin cewa an gano kudaden cikin dan kamfen wanda ake zargin.

Ya ce laifin ya sabawa sashi na 287 na Dokar Masu Laifi na Jihar Legas ta 2015 (Da aka yi wa kwaskwarima).

Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa (NAN) ta ruwaito cewa idan an tabbatar da laifinsa a karkashin sashi na 287, kotu za ta iya tura wanda ake zargin gidan yari na shekaru uku.

Alkalin kotun, Oluwatoyin Ojuromi ta bayar da belin wanda ake zargin kan kudi N30,000 da mutane biyu da za su tsaya masa.

Ojuromi ta ce dole daya daga cikin wadanda za su tsaya masa ya kasance dan uwa na jini.

Ta dage cigaba da sauraron shari'ar zuwa ranar 19 ga watan Augustan 2019.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel