Jibrin ya kore jita-jitan samun sabani da Gbajabiamila bayan kin sanya sunansa a nade-naden kwamiti (hotuna)

Jibrin ya kore jita-jitan samun sabani da Gbajabiamila bayan kin sanya sunansa a nade-naden kwamiti (hotuna)

- Kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila a ranar Alhamis, 25 ga watan Yuli ya sanar da sunayen kamitocin majalisar

- Ba a ambaci sunan babban dan kashenin Gbajabiamila, Abdulmumin Jibrin cikin shugabannin kwwamitin ba inda hakan ya kawo rade-radin cewa akwai sabani a tsakaninsu

- Sai dai Jibrin ya kore jita-jitan bayan wata ganawar sirri da suka yi da Gbajabiamila

Kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila a ranar Alhamis, 25 ga watan Yuli ya sanar da sunayen kamitocin majalisar.

Abun mamaki sai gashi babu sunan babban dan kashenin Gbajabiamila, Abdulmumin Jibrin cikin shugabannin kwwamitin ba inda hakan ya kawo rade-radin cewa akwai sabani a tsakaninsu.

Sai dai kuma Jibrin ya kore jita-jitan bayan wata ganawa tare da Gbajabiamila wanda ya kai masa ziyara gidansa na Abuja.

KU KARANTA KUMA: Har yanzu mahaifiyar Leah Sharibu bata yanke kauna da dawowar ‘yarta ba

“Ina rakiya ga kakakin majalisa zuwa wajen motarsa bayan wani ziyarar bazata da safen nan. Mun sanar da shugabannin kwamitoci sannan mun yi bakin kokarinmu wajen tabbatar da adalci da duba cancanta.

“Kamar koda yaushe kakakin majalisa ya fuskanci matsin lamba sosai amma ya nuna karfin gwiwa. Tarihi zai yi adalci a gare shi. Allah ya taimaki majalisa ta tara."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel