Hukumar WAEC ta saki jarrabawar bana

Hukumar WAEC ta saki jarrabawar bana

Hukumar shirya jarrabawar kammala karatun sakandire a yankin Yammacin Afirka, WAEC (West African Examination Council), ta saki sakamakon jarrabawar bana da aka gudanar a tsakanin watan Mayu da Yunin 2019.

Wannan sabon rahoto ya zo ne a cikin wata sanarwa daga bakin kakakin hukumar WAEC na kasa, Mista Demianus Ojijeogu ya gabatar a ranar Alhamis yayin ganawa da manema labarai.

Mista Ojijeogu ya ce dalibai da suka zana jarrabawar a bana za su iya fara duba sakamakon su a ranar Juma'a 26 ga watan Yulin ta hanyar amfani da lambobin su na jarrabawa a kan shafin ta na yanar gizo.

A wani rahoton mai nasaba da wannan, hukumomi a Najeriya sun dade suna kokawa kan yadda dalibai ke satar jarrabawa musamman wadanda ake a kasa baki daya kamar NECO, WAEC da kuma JAMB.

KARANTA KUMA: Firaiministocin Birtaniya 13 da suka yi zamani da sarauniyar Ingila, Elizabeth

Kamar yadda shafin BBC Hausa ya ruwaito, satar jarrabawa ta zama ruwan dare a Najeriya kuma hukumomi masu ruwa da tsaki na daukar matakai domin dakile wannan annoba da ta zamto tamkar al'ada a tsakanin dalibai musamman na sakandire.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel