Har yanzu mahaifiyar Leah Sharibu bata yanke kauna da dawowar ‘yarta ba

Har yanzu mahaifiyar Leah Sharibu bata yanke kauna da dawowar ‘yarta ba

Har yanzu Misis Rebbeca Sharibu, uwar yarinyar makarantar sakandare na Dapchi, Leah Sharibu, tayi imani game da dawowar ‘yarta a raye.

Da take martani akan bidiyon da Boko Haram suka saki inda wata ma’aikaciyar agaji, Grace, tayi kira ga kungiyar Kiristocin Najeriya da hukumar yaki da yunwa, kungiyoyi masu zaman kansu da ke aiki a jihar Borno, kan su ceto ya kafin a kashe ta kamar yadda aka kashe Alice da Leah Sharibu.

A cewar Misis Sharibu, “duk tsawon lokaci da zai dauka, fatana shine cewa har yanzu yata na raye kuma zata dawo a raye daga hannun Boko Haram. Har yanzu ina duba ga wannan ranar sannan ina da tabbacin cewa za ta dawo.”

Misis Sharibu ta bayyana cewa ita bata ma ga bidiyon da ke yawo ba.

Ta jadadda kira ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari da yayi duk abunda ya kamata domin ceto ‘yarta, kamar yadda take kuma rokon mutanen da ke rike da ‘yarta da su sake ta ba tare da takunkumi ba.

KU KARANTA KUMA: Wasu kayayyaki da sojoji suka kama sun sake tona asirin 'yan kungiyar ISWAP - ONSA

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Fadar Shugaban kasa, a daren ranar Alhamis, 25 ga watan Yuli, tayi martani akan wani bidiyo Boko Haram da ke yawo, wanda ya nuna wasu ma’aikatan agaji da yan ta’addan suka sace sannan wanda a ciki aka yi ikirarin cewa an kashe Leah Sharibu, daya daga cikin yan makaranta da aka sace a jihar Yobe.

A wani dan takaitaccen jawabi, kakakin Shugaban kasa Muhammadu Buhari, yace an sanar da fadar Shugaban kasa game da bidiyon.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel