Firaiministocin Birtaniya 13 da suka yi zamani da sarauniyar Ingila, Elizabeth
A halin yanzu kasar Birtaniya ta na da tsaffin Firaiministoci 76 kamar yadda gwamnatin kasar ta bayyana a shafinta na yanar gizo.
A ranar Laraba 24 ga watan Yulin 2019, Mista Boris Johnson, ya karbi ragamar jagorancin kasar Birtaniya a matsayin Firaiministan ta na 77 a tarihi.
Cikin wannan jeri, sauraniyar Ingila, Elizabeth II, ta yi zamani da tsaffin firaiministoci 13 tsawon shekaru 66 da take ci gaba da shafewa a kan gado na mulki.
Mista Boris, sabon Firaiministan kasar da aka rantsar, shi ne cikon na 14 da zai yi zamani guda tare da sarauniyar Ingila.
KARANTA KUMA: Zababbun ministoci 8 da majalisar dattawa za ta tantance a ranar Juma'a
Ga jerin Firaiministocin da suka yi zamani da Sarauniya Elizabeth cikin tsawon shekaru 66 da suka shude tun bayan hawanta gado na sarauta a ranar 2 ga watan Yunin 1953:
- Wiston Churchill: Ya kasance Firaiminista daga shekarar 1940 zuwa 1945 da kuma tsakanin shekarar 1951 zuwa 1955. Shekaru biyu cikin wa'adin gwamnatin Churchill na biyu, sarauniya Elizabeth ta ci gajiyar masarautar Ingila.
- Anthony Eden (1957 - 1963)
- Harold Macmillan (1957 - 1963)
- Alec Douglas Home (1963 - 1964)
- Harold Winson (1964 - 1970) da kuma (1974 - 1976)
- Edward Heath (1970 - 1974)
- James Callaghan (1976 - 1979)
- Margaret Thatcher (1979 - 1990)
- John Major (1990 - 1997)
- Tony Blair (1997 - 2007)
- Gordon Brown (2007 - 2010)
- David Cameron (2010 - 2016)
- Theresa May (2016 - 2019).
Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
https://facebook.com/legitnghausa
https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng