Da duminsa: Buhari ya tashi zuwa Monrovia

Da duminsa: Buhari ya tashi zuwa Monrovia

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya tashi zuwa Liberia domin halartar bikin taya kasar murnar bikin cika shekaru da 172 da samun 'yanci da kuma karbar wata kyauta ta musamman.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun kakakin shugaban kasa, Garba Shehu, wacce ta fito daga fadar shugaban kasa a yammacin ranar Alhamis.

Ana sa ran dawowar shugaba Buhari ranar Juma'a.

Jawabin ya ce, "shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya bar Abuja zuwa Monrovia (babban birnin kasar Liberia) domin halartar bikin taya kasar murnar cika shekaru 172 da samun 'yanci.

"Bayan kasancewarsa babban bako a wurin taron, shugaba Buhari zai karbi kyautar girmamawa mafi daraja da kasar Libria ke bawa mutane masu daraja.

"Gwamnatin kasar Liberia ce ke bayar da kyautar ga mutane masu daraja da suka taka muhimmiyar rawa a harkokin kasa da kasa, gwamnati, addini, kimiyya, kasuwanci, aikin jin kai da jarumta da sadaukar wa da makamantansu."

Kazalika, sanarwar ta ce shugaba Buhari ya samu rakiyar gwamoni da suka hada da; Kayode Fayemi na jihar Ekiti, Abdulrahman Abdulrazaq na jihar Kwara, Mai Mala Buni na jihar Yobe, da kuma sakataren ma'aikatar harkokin waje, Ambasada Mustapha Sulaiman, da sauran manyan kusoshin gwamnati.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng