Kasar Iran ta nemi a aike mata da Zakzaky domin yi masa magani

Kasar Iran ta nemi a aike mata da Zakzaky domin yi masa magani

Lauyan kolu na kasar Iran, Muhammad Montazeri, ya nemi gwamnatin tarayyar Najeriya da kuma hukumar shari'a ta kasar da su bai wa jagoran mabiya akidar shi'a, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky, damar zuwar kasar Iran domin a duba lafiyarsa.

A cewar kamfanin sadarwar na Ahlul Bait, wata kafar watsa labarai mai tushe a kasar Iran, Montazeri ya bayyana hakan ne cikin wata wasika a ranar Asabar da ta gabata.

Jami'in na kasar Iran ya kuma nemi hukumar shari'a wadda ta kasance uwa mabada mama wajen karbar koke da tabbatar da hakki, da ta bayar da belin Sheikh Zakzaky da ya kasance jagoran kungiyar IMN Islamic Movement of Nigeria da aka fi sani da kungiyar shi'a ta Najeriya.

Montazeri ya kuma soki gwamnatin tarayyar Najeriya dangane da yadda take tafiyar da sha'anin 'yan shi'a a kasar yayin da ya bayyana damuwa a kan yadda rashin lafiyar jagoran na IMN ke ci gaba da ta'azzara gami da kaiwa mataki na intaha ba tare da kulawa ba.

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa, Sheikh Zakzaky wanda bai haura shekaru sittin ba a duniya, ya rasa idon sa daya na bangaren hagu a yayin da dakarun tsaro suka kai wani simame Arewacin garin Zazzau da aka fi sani da Zaria fiye da shekaru uku da suka gabata.

Dakarun tsaro sun kai simame biyo bayan cin kashi da wulakantaswa da mabiya akidar shi'a suka yiwa shugaban hafsin sojin kasan Najeriya, Laftanar Janar Tukur Buratai, yayin da yayi yunkurin wucewa ta wata hanya a garin Zaria tare da tawagar sa.

Wannan lamari ya janyo salwantar rayukan mabiya shi'a da dama da suka hadar da 'ya'yan Sheikh Zakzaky guda uku a sakamakon tarzomar da ta biyo baya.

KARANTA KUMA: Ministoci: Majalisar dattawa ta tantance Aliyu, Shehuri, Magashi da wasu zababbu hudu

Cikin tsawon shekaru biyu da suka gabata, mabiya akidar shi'a ba su gushe ba wajen gudanar da zanga-zangar adawa a garin Abuja a kan ci gaba da tsare jagoransu da hukumar kasar ke yi tare da kiraye-kiraye na gaggauta sakin sa.

Zanga-zangar da suka gudanar a kwana-kwanan ta yi matukar muni yayin da rayukan mutane fiye da goma suka salwanta da suka hadar har da jami'an tsaro na 'yan sanda da kuma manema labarai.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel