Yanzu-yanzu: An sako matan da akayi garkuwa da su a Kagara

Yanzu-yanzu: An sako matan da akayi garkuwa da su a Kagara

An sako surukar Shugaban ma'aikatan fadan gwamnan jihar Niger, Alhaji Abubakar Sani Bello da wasu mata da 'yan bindiga suka yi awon gaba da su a garin Kagara na jihar Niger kamar yadda The Nation ta ruwaito.

An ruwaito cewa an saki matar a wani jiha ne da ke da nisa da Niger bayan an biya masu garkuwa da mutanen kudin fansa.

Sai dai dukkan wadanda abin ya shafa ba su amsa cewa an biya kudin fansa ba duk da cewa wani na kusa da iyalansu ya fadi cewa an biya kudin fansa kafin aka sako su.

DUBA WANNAN: Adamu Adamu ya fadi aikin da ya yi wa Buhari a baya tun kafin ya nada shi minista

Anyi kokarin ji ta bakin daya daga cikin mazan matan da akayi garkuwa da su, Injiniya Ojukaiye amma wayarsa tana kashe.

An kuma bayyana cewa a halin yanzu ana duba lafiyar matan sakamakon jigatar da su kayi a hannun masu garkuwar da su.

Da aka tuntube shi, Kakakin 'Yan sanda na jihar, Abubakar Muhammad ya ce har yanzu suna kokarin ganin yadda za a ceto matan.

Ya ce idan an samu wani labari game da matan, za a sanar da kafafen yadda labarai.

Idan ba manta ba kimanin mako guda da ta gabata, wasu 'yan bindiga sun yi awon gaba da surukar shugaban ma'aikatan fadar gwamnatin jihar Niger, Ibrahim Balarabe da wasu mata a garin Kagara.

Mazaje sauran matan biyu jami'ai na musamman ne na Hukumar Kiyaye Haddura ta Kasa (FRSC) a Kagara.

'Yan bindigan sun shigo garin suna ta harbe-harbe kafin daga bisani suka yi awon gaba da matan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164