Gwamnan Kano ya biya bashin N2,000,000,000 da ake bin daliban Kano a jami’ar Sudan

Gwamnan Kano ya biya bashin N2,000,000,000 da ake bin daliban Kano a jami’ar Sudan

Gwamnan jahar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya biya bashin kimanin kudi naira biliyan biyu da jami’ar El-Razi take bin daliban jahar Kano dake karatu a jami’ar a kasar Sudan, inji rahoton kamfanin dillancin labaru, NAN.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito jami’ar El-Razi ta dade tana bin gwamnatin jahar Kano wannan bashi, tun zamanin tsohon gwamnan Rabiu Kwankwaso, har sai a wannan lokaci da Gwamna Ganduje ya biya wadannan kudade.

KU KARANTA: Zainab da da Mahmud: Bayani game da sabbin ministoci daga jahar Kaduna

Ganduje ya sanar da biyan kudin ne yayin daya karbi bakuncin shugaban kwamitin gudanarwar jami’ar, Farfesa Ibrahim Ghandour a ranar Talata, 23 ga watan Yuli a fadar gwamnatin jahar Kano inda yace ya ci gadon bashin ne daga tsohuwar gwamnati.

“Gwamnatina ta tarar da wanna bashi ne daga tsohuwar gwamnati, amma mun samu daman biyan wannan bashi sakamakon tattaunawa tsakanin hukumar jami’ar da gwamnatin Kano, domin dalibanmu su kammala karatunsu ba tare da matsala ba.” Inji Ganduje.

Ganduje wanda ya samu wakilcin mataimakin gwamnan jahar, Dakta Nasiru Gawuna ya bayyana cewa gwamnatinsa ta biya kashi 80 na kudin makarantar daliban Kano dake India, Misra da Cyprus, inda yace a jami’ar Cyprus kadai sun biya sama da naira miliyan 300.

A nasa jawabin, shugaban jami’ar El-Razi, Farfesa Ibrahim Ghandour ya bayyana cewa sun kawo ziyara jahar Kano ne domin bayyana godiyarsu tare da jin dadin mu’amalar dake tsakaninsu da gwamnatin Kano.

“Hakazalika muna neman mai girma gwamna ya amince da bukatarmu ta karramashi da lambar girmamawa ta Dakta daga jami’armu, a yanzu jami’ar El-Razi ta cika shekara 23, kuma mun yaye likitoci da dama, amma wannan Dakta da zamu baka babu wanda ya taba samunta.” Inji shi.

Daga karshe Gwamna Ganduje ya bayyana godiyarsa bisa wannan girmamawa da jami’ar ta yi alkawarin yi masa, a ranar 26 ga watan Agustan 2019 ne za’a karrama Ganduje a kasar Sudan.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel