Zainab da da Mahmud: Bayani game da sabbin ministoci daga jahar Kaduna

Zainab da da Mahmud: Bayani game da sabbin ministoci daga jahar Kaduna

Zuwa yanzu rahotanni sun gama karade kafafen watsa labaru game da jerin sunayen mutanen da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aika ma majalisa wadanda yake muradin nadawa mukamin ministoci a sabuwar gwamnatinsa.

Sunayen sun hada da tsofaffin ministocinsa da suka yi tare daga 2015 zuwa 2019, akwai kuma tsofaffin gwamnoni, tsofaffin Sanatoci da kuma sabbin fuskoki da dama wadanda sune suka fi yawa, kamar yadda Legit.ng ta gano.

KU KARANTA: Idan ajali ya yi kira: Wani Mutumi ya fado daga benen Kotu ya mutu murus

Zainab da da Mahmud: Bayani game da sabbin ministoci daga jahar Kaduna
Zainab da da Mahmud: Bayani game da sabbin ministoci daga jahar Kaduna
Asali: Facebook

Sai dai akwai wasu jahohi da shugaba Buhari ya zabi mutane biyu biyu daga cikinsu don nadasu ministoci, jahohin nan suna hada da Anambra, Kaduna, Kano, Legas, Bauchi, Edo, da kuma jahar Kwara. A yanzu ga wani takaitaccen bayani game da wakilan jahar Kaduna dake cikin jerin sunayen.

1- Zainab Shamsuna Ahmad

An haifi Zainab ne a ranar 16 ga watan Yunin 1960, kuma ta yi karatu a sakandarin Queen Amina a 1977, sa’annan ta garzaya jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria inda ta yi karatu a ilimin kididdiga a 1981, sa’annan ta yi digir na biyu a jami’ar jahar Ogun a 2004.

Zainab ta fara aiki a ma’aikatar kudi ta jahar Kaduna a shekarar 1982, sa’annan ta koma kamfanin sadarwar ta NITEL a 1985 har zuwa 2009, a shekarar 2010 aka nadata shugaban hukumar hakar ma’anan kasa ta Najeriya, daga bisani Buhari ya nadata karamar ministar tsare tsare da kasafin kudi, a 2018 kuma ya nadata ministar kudi.

2- Muhammad Mahmood Abubakar

Tsohon aminin shugaban kasa Muhammadu Buhari ne, wanda aka haifeshi a unguwar Tudun wada Kaduna, jahar Kaduna, kuma ya yi aiki tare da shugaba Buhari tun a hukumar PTF, haka zalika ya taba zama dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar ta kudu a majalisar wakilai karkashin tutar jam’iyar APP da ANPP. A yanzu haka shine shugaban majalisar gudanarwa ta hukumar ilimi ta bai daya, UBEC.

Shine mutumin da yan bindiga suka yi garkuwa dashi da diyarsa a kwanakin baya a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel