Allah mai iko: An shiga rudani a kasar Indiya bayan an shafe watanni uku ba a haifi mace ba
- Wani bincike da aka gabatar a kasar Indiya ya kawo rudani da tsoro a zukatan al'ummar kasar bayan sun gano wani sabon al'amari
- Mahukunta a kasar sun gano cewa a cikin watanni uku da suka gabata a kauyuka 132 ba a haifi mace ko daya ba a cikin yara 216 da aka haifa a fadin kauyukan
- Yanzu dai manyan jihar sun bukaci hukumomin lafiya da su yi binciken gaggawa kuma su nemo ainahin dalilin da yasa hakan take faruwa a yankin
Mahukunta a kasar Indiya sun nuna damuwarsu, bayan an gano cewa a cikin yara 216 da aka haifa a kauyuka 132 na wata jiha a kasar ta Indiya cikin watanni uku da suka gabata babu mace ko daya a ciki.
Manya a jihohin Uttarkashi da Uttarakhand sun nemi su san dalilin da yake kawo wannan lamari, sun zargi cewa iyaye suna zubar da ciki ne idan suka fuskanci cewa dan dake cikin ba namiji bane.
A yanzu dai an sanya alamar tambaya akan mutanen wadannan kauyuka 132, hakan na nufin za a sanya ido sosai akan mutanen da za a dinga haifa a wadannan kauyuka.
KU KARANTA: Tonon silili: An kama wani ma'aikacin banki yana kokarin yin zina da wata budurwa a cikin banki
"Akwai abin tsoro ace a cikin kauyuka 132 ba a samu haihuwar 'ya mace ba," in ji wani dan majalisa mai suna Gopal Ravat.
"Na umarci hukumar lafiya ta binciko ainahin abinda ya kawo wannan matsalar, kuma suyi gaggawar nemo mafita," in ji Ravat, ya kara da cewa gwamnati tana shirin gabatar da wani shiri na wayar da kan jama'a akan wannan lamari.
An gabatar da kidaya a kasar Indiya a shekarar 2011 an kuma gano cewa akwai tazara a wajen haihuwa, inda ake samun mata 943 da kuma 1000 a fadin kasar.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng