Janar Magashi: Abinda ya kamata ku sani game da zababben ministan Buhari daga jihar Kano

Janar Magashi: Abinda ya kamata ku sani game da zababben ministan Buhari daga jihar Kano

Manjo Janar Bashir Salihi Magashi (murabus) yana daya daga cikin mutanen da Shugaba Muhammadu Buhari ya zaba daga jihar Kano domin yi wa nadin mukamin minista.

An nada magashi a matsayin gwamnan jihar Sokoto daga watan Augustan 1990 zuwa Janairun 1992 yayin zamanin mulkin shugaban kasa na soji, Janar Ibrahim Badamasi Babangida.

Magashi ya yi digiri a fanin koyon aikin lauya daga Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria. Ya kuma samu lambar karramawa ta kasa wato CFR.

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: An sake yin gumurzu tsakanin jami'an tsaro da 'Yan Shi'a a Abuja

An bawa Magashi Rundunar Sojoji ta Brigade of Guards a watan Satumban 1993 domin ya jagorance su a lokacin da ake gumurzun ganin Janar Sani Abacha ya zama shugaban kasa. Yana daya daga cikin na hannun daman Abacha da suka yi nazari kan zaben June kuma daga bisani aka soke zaben a 2003.

Jim kadan bayan kasar ta koma mulkin Demokuradiyya, gwamnati ta yi wa manyan sojoji da suka yi aiki na tsawon sama da watanni shida murabus na tilas cikin su har da Manjo janar Bashir Magashi.

A shekarar 2002, an nada shi mai bayar da shawara kan fanin shari'a na jam'iyyar All Nigeria People’s Party ANPP. A watan Afrilun 2007, Magashi ne dan takarar gwamna na jam'iyyar Democratic People’s Party (DPP) a jihar Kano.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags: