Da duminsa: PDP tayi tsokaci kan sunayen sabbin ministocin Buhari

Da duminsa: PDP tayi tsokaci kan sunayen sabbin ministocin Buhari

Babban jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) a ranar Talata ta yi tsokaci kan jerin sunayen ministocin da Shugaba Muhammadu Buhari ya mika wa Majalisa domin tantancewa idan ta ce babu wani alamar cewa za a samu cigaba ko sauki a karkashin gwamnatin APC.

A cikin sanarwar da Sakataren Yada Labarai na kasa na jam'iyyar, Kola Ologbonidiyan ya fitar, ya ce 'yan Najeriya sun yi bakin cikin ganin an sake mika sunayen wasu tsaffin ministoci da ba su tabbuka komai a ma'aikatatunsu ba.

Wani sashi cikin sakon da PDP ta fitar ya ce, "Jam'iyyar da ba jama'a suka zabe ta bane kawai za ta iya fitar da irin wannan sunayen ministocin. Sun ce wannan bata lokaci ne domin ba za su iya gudanar da ayyukan da 'yan Najeriya ke bukata ba.

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: An sake yin gumurzu tsakanin jami'an tsaro da 'Yan Shi'a a Abuja

"Sake zaben tsaffin ministocin da su kayi aiki a zangon mulkinsa na farko ya nuna cewa Buhar da APC ba su da hangen nesan da za su fitar da Najeriya daga cikin mawuyacin halin talauci da rashin tsaro da suka jefa ta cikin shekaru hudu da suka gabata.

"Kamata ya yi shugaba na gari ya tuntubi 'yan Najeriya kafin tattara sunayen ministoci duba da halin da kasar ke ciki.

"Idan da gaske gwamnati ke yi, ba za ta cika jerin sunayen da mutanen da suka taimaka wurin cin hanci da rashawa ba tare da kare mutanen da suka karkatar da kudade domin yin kamfe din Buhari a zaben 2019.

"Wani abin mamaki kuma shine babu matasa cikin jerin sunayen ministocin duk da cewa su ne manyan gobe."

Sanarwar ta kuma cigaba da cewa hanya daya da Najeriya za ta fito daga cikin kangin tatattalin arziki da kallubalen tsaro da ta shiga shine idan Atiku Abubakar ya karbo nasararsa da aka sace a kotun zabe.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel