Buhari ya saki sunayen ministoci ne don kawar da tunanin jama'a - kakakin Atiku

Buhari ya saki sunayen ministoci ne don kawar da tunanin jama'a - kakakin Atiku

Paul Ibe, Mai magana da yawun tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar a ranar Talata ya yi zargin cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya fitar da sunayen ministocinsa ne domin ya kawar da tunanin al'umma daga gumurzun da 'Yan sanda su kayi da 'Yan Shi'a a Abuja.

A wani rubutu da ya wallafa a shafin Twitter a ranar Talata, Kakakin Atikun ya ce shugaban kasa ya yi amfani da jerin sunayen ministocinsa 43 domin kawar da hankulan mutane daga mummunar abinda ya faru na mutuwar mutane 13 yayin zanga-zangar da 'Yan Shi'a su kayi a Abuja.

Mr Ibe ya rubuta "Buhari ya fitar da jerin sunayen ministocinsa ne domin kawar da hankulan mutane daga mutuwar mutane su kayi yayin zanga-zangan da 'Yan Shi'a suka gudanar a ranar Litinin."

DUBA WANNAN: Dalilin da ya sa Arewa ke hakuri da Buhari - Shehu Sani

A dai ranar Talata ne shugaban kasar ya aike da sunayen mutane 43 zuwa ga majalisar dattawa domin tantancewa.

Tsaffin ministocin Buhari ba su da yawa cikin jerin sunayen da aka aike wa majalisar, wasu daga cikinsu sun hada da Chris Ngige, Hadi Sirika, Rotimi Amaechi, Adamu Adamu, Mohammed Adamu, Babatunde Fashola da Lai Mohammed.

Sauran wadanda sunayensu ya fito sun hada da Uche Ogah, Emeka Nwajuiba, Sadiya Farouk, Musa Bello, Godswill Akpabio, Sharon Ikeazor, Ogbonnaya Onu, Akpa Udo da Adebayo (Ekiti).

Har ila yau, akwai su Timipre Sylva, Adamu Adamu, Shewuye (Borno), Isa Pantami, Gbemi Saraki, Ramatu Tijani, Clement Abam, Paullen Tallen, Abubakar Aliyu, Sale Mamman, Abubakar Malami, Muhammed Mamood, Rauf Aregbesola, Mustapha Buba Jedi Agba, Olamilekan Adegbite da Mohammed Dangyadi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel