Wata sabuwa: Za a hana kallon fina-finan kasashen waje a Najeriya - Dan majalisa

Wata sabuwa: Za a hana kallon fina-finan kasashen waje a Najeriya - Dan majalisa

- Dan wasan fina-finan Nollywood yayi kira da a hana kallon fina-finan kasashen waje a Najeriya

- Jaruminb ya bayyana cewa hakan ita ce hanya daya da ta rage da za a iya kawo cigaba a bangaren harkar fina-finai a kasar nan

- Ya bayyana cewa dolene gwamnatin tarayya ta sanya kwakkwarar doka da zata hana shigo da fina-finan daga wasu kasashe domin na cikin gida su habaka

Dan wasan fina-finan kudancin Najeriya na Nollywood, kuma dan siyasa a jihar Legas, Desmond Elliot yayi kira da a hana kallon fina-finan turawa dana kasashen waje a Najeriya, inda ya bayyana cewa hakan itace hanya daya da za'a kawo cigaba a bangaren fina-finai a Najeriya.

Jarumin mai shekaru 45, wanda yake wakiltar mazabar Surulere a majalisar jihar Legas, ya bayyana hakan aa wata hira da yayi da gidan talabijin na HIP, a lokacin da yake magana akan yanayin koma bayan da ake samu a bangaren shirin fina-finai a kasar nan.

KU KARANTA: To fah: Ni talaka ne ku taimaka ku saki mahaifiyata - Samson Siasia ya roki wanda suka yi garkuwa da mahaifiyarsa

A cewar shi, gwamnatin tarayya ta sanya doka mai tsauri wurin shigo da fina-finai daga wasu kasashen, domin kuwa hakan ne kawai hanya daya da za a samu cigaba a bangaren fina-finai a kasar nan.

Idan ba a manta ba makonnin da suka gabata mun kawo muku rahoton yadda fitaccen jarumin barkwancin nan na wasan Hausa wanda aka fi sani da Sulaiman Bosho ya bayyana cewa yanzu mutane na shiga harkar fim ne kawai domin samun kudin sanyawa a aljihu, ba wai suna shiga domin kishi ba ne.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel