Tonon silili: An kama wani ma'aikacin banki yana kokarin yin zina da wata budurwa a cikin banki

Tonon silili: An kama wani ma'aikacin banki yana kokarin yin zina da wata budurwa a cikin banki

- Asirin wasu ma'aikatan banki dake aiki a bankin jami'ar jihar Legas ya tonu, bayan an hango su suna shirin aikata lalata a cikin ofis

- An hango namijin dai da macen a cikin ofis suna cirewa junansu kaya a wani bidiyo da wani mutumi ya sanya a shafinsa na twitter

- Wannan bidiyo ya kawo cece-kuce, yayin da wasu suke ganin a cire mutumin daga aikin shi, inda wasu kuma suka dinga rokar mutumin ya cire bidiyon domin rufawa mutumin asiri

Wani bidiyo da yake yawo a shafin sada zumunta na Twitter wanda wani mai amfani da shafin mai suna PrinceEbuka ya yada, ya nuna lokacin da wasu ma'aikatan bankin jami'ar Legas su biyu suke kokarin yin lalata a lokacin da suke aikin dare a bankin.

A bidiyon, an gano mace da namiji, suna cirewa junansu kaya a cikin ofis, daga baya kuma aka hango namijin ya hau ya zauna akan kujera ya jawo macen.

KU KARANTA: To fah: Ni talaka ne ku taimaka ku saki mahaifiyata - Samson Siasia ya roki wanda suka yi garkuwa da mahaifiyarsa

Sai dai kuma bidiyon ya jawo cece-kuce a shafukan sada zumuntar, inda wasu suke kira da a cire ma'aikacin, wasu kuma suna kira da a cire bidiyon domin rufawa ma'aikacin asiri.

Wannan lamari yana daya daga cikin dalilan da wasu suke ganin bai kamata a dinga kyale 'ya mace ta dinga zuwa aiki ba, saboda irin wannan abubuwan da suke faruwa a wajen aiki ba tare da sanin iyaye ko mazajensu ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel