An gano kasar da ya fito: Mutumin da ya dare jirgin sama ya hana shi tashi a Legas ba dan Najeriya ba ne - FAAN

An gano kasar da ya fito: Mutumin da ya dare jirgin sama ya hana shi tashi a Legas ba dan Najeriya ba ne - FAAN

Hukumar kula da filayen tashi da saukar jiragen sama na Najeriya (FAAN) ta ce mutumin nan da ya dare fuka-fukan jirgin saman kamfanin Azman tare da hana shi tashi a filin jirgin sama na Murtala Mohammed dan asalin kasar Nijar ne, ba Najeriya ba.

Fasinjojin da ke cikin jirgin saman da zai kai su Fatakwal, jihar Ribas, sun shiga halin dimuwa bayan sun hango mutumin mai suna Usman Adamu ya yi dare-dare a kan daya daga cikin fuka-fukan jirgin da suke ciki yayin da ya ke niyyar tashi sama.

Takaitaccen faifan bidiyon Adamu yayin da ya dare fuffuken jirgin ya watsu a dandalin sada zumunta da kafafen yada labarai na gida da na waje.

Adamu ya yi yunkurin shiga dakin ajiye kaya na jirgin, lamarin da ya tilasta direban jirgin kashe injin jirgin, ya kuma fasa tashi sama kamar yadda ya yi niyya da farko.

Janar manajan FAAN da jami'in hulda da jama'a, Henrietta Yakubu, sun tabbatar da cewa mutumin dan asalin kasar Nijar ne da hukumar ta kama kwana biyar da suka wuce saboda yin kutse a filin jirgin sama.

DUBA WANNAN: Kasashen duniya 10 da mata suka fi maza yawa

Da ya ke gana wa da manema labarai a Kano, Kaftin Rabi'u Hamisu Yadudu, babban manajan FAAN, ya bayyana cewa jami'an tsaro sun kama Adamu a filin jirgin yayin da suke gudanar da faturu, kwanaki biyar da suka gabata.

Wata majiya a filin jirgin sama na Legas ta ce yanzu haka mutumin na amsa tambayoyi kuma ana gudanar da bincike a kansa, da ya hada da binciken lafiyar kwakwalwarsa.

Kakakin rundunar 'yan sandan da ke filin jirgin, Mista Joseph Alabi, ya tabbatar da cewa an damka mutumin a hannunsu kuma suna gudanar da bincike a kansa.

Tuni hukumar FAAN ta dakatar da manyan shugabannin bangaren tsaro su hudu har zuwa lokacin da za a kammala binciken yadda aka yi sakaci har mutumin ya kai ga zuwa wurin da jirgi ke tashi tare da dare fuffukensa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel