Tirkashi: Wasu ma'aurata da suka shafe shekara goma basu taba kwanciya da juna ba

Tirkashi: Wasu ma'aurata da suka shafe shekara goma basu taba kwanciya da juna ba

- Yanzu wasu mazan zasu yi tunanin ba zai taba yiwuwa ba, daga yaya mutum zai rayu shekara goma da yin aure ba tare da saduwa da juna ba

- James ya yiwa kanshi alkawarin cewa ba zai taba saduwa da mace ba har sai bayan yayi aure, kuma matarshi ce mace ta farko da zai fara sani a matsayin 'ya mace

- Sai dai kuma ba hakan lamarin ya zo musu ba shi da matar shi Michaela bayan sun shafe watanni 21 suna jira suyi aure

Tun yana dan shekara 14 James yasha alwashin cewa ba zai taba sanin 'ya mace ba har sai yayi aure kuma yayi alkawarin matarshi ce mace ta farko da zai fara kwanciya da ita bayan an daura musu aure, James ya bayyana hakan a matsayin hanya mafi dacewa.

Michaela da James sun jira na tsawon watanni 21 suyi aure a cikin darensu na ranar farko, abin bai zai musu yadda suke tunani ba.

Micheala da James sun wallafa labarinsu a wani shafi mai suna Found Me. A cikin rubutun na su sun bayyana yadda yawon amarcin su yayi musu dadi, duk da dai Mrs. Reece ba ta taba kwanciya da namiji ba, kuma shekarunta 25.

Mrs Reece na da wata cuta mai suna 'Vaginismus, kuma take hana ta saduwa da mijinta.

KU KARANTA: Tsegumi: Ali Nuhu zai zama ministan wasanni da matasa a gwamnatin Buhari

Masana a bangaren lafiya sun bayyana cewa babu maganin irin wannan cutar wacce take hana ta saduwa da mijin nata.

Sanadiyyar cutar Michaela ma'auratan sun yi kokarin zama na tsawon shekaru tara ba tare da sun sadu da juna ba.

Michaela da James sun kasa samun maganin wannan cutar saboda babu ita a kasar Australia. Ma'auratan sun bude wani shafi na neman taimako wanda zai taimaka musu su samu isasshen kudin da zasu je kasar New York don nema mata magani.

Tafiyar ta su zata ci kimanin Dala dubu 25, amma suna fatan samun koda Dala dubu 15 ne a shafinsu.

Michaela da James dai suna fatan zuwa kasar New York don yi mata magani a watan Oktoba.

Duk wannan abu da ke faruwa James bai taba nuna gajiyawar shi ga Michaela ba kuma ya tsaya da ita na tsawon wannan shekarun.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel